Daga Ukasha Idris
‘Yan’uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Da’irar Bauchi sun kai ziyarar ta’aziyya da jajantawa ga iyalai da almajiran Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa babban rashin Jagora da aka yi.
Wakilin ‘yan’uwa na Da’irar Bauchi, Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ne ya jagoranci tawagar yayin ziyarar da ya gudana a babban masallacin marigayin da ke unguwar Maƙera a cikin garin Bauchi a ranar Lahadi.

Da yake jawabin jajantawa, Sheikh Yashi ya nuna cewa rasuwar Sheikh Ɗahiru babban rashi ne sosai da addinin Musulunci ya yi, ya nuna irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban addini da horas da mahaddata Alƙur’ani a sassa daban-daban na Nijeriya da ma Afrika.
Ya ƙara da cewa a ɓangaren ‘yan’uwa akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky, inda ya ce a lokuta daban-daban idan Shaikh Zakzaky ya zo jihar Bauchi yana yawan zuwa har gidan Sheikh Ɗahiru domin gaida shi.
Ya kuma nuna cewa jagororin biyu suna da kyakkyawar alaƙa da burin ganin an ciyar da addinin Musulunci gaba a kowane lokaci.

Ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa da gafara, ya albarkaci zuri’ar da ya bari.
Daga cikin tawagar da suka rufa wa Sheikh Yashi baya, akwai Malam Aliyu Dawud Azare, Shaikh Ishaƙ Misau da Malam Aliyu Yusuf Darazo da wakilan ‘yan’uwa na da’irori da garuruwa daban-daban.

Babban ɗan Sheikh Ɗahiru, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi shi ne ya amshi tawagar ‘yan’uwa a wajen ziyarar.
Da yake magana kan dubban jama’a da suke ta kawo musu ziyarar jajantawa, Sheikh Ibrahim ya gode, tare da nuna cewa hakan ya sake tabbatar musu da cewa mahaifinsu ya zauna da kowa lafiya.
A lokacin da tawagar Shugaban Ɗariƙar Ƙadiriyya, Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara ya kawo musu ziyara, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi ya tunatar da al’ummar Musulmi da kada su bari a raba kansu. Ya ce yanzu ne lokacin da ya dace a ƙara haɗa kai domin ci gaban addinin Musulunci.
Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata bayan fama da jinya.






