Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana rasuwar mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda na ƙasa mai ritaya DIG Abdulƙadir Ɗanwawu Fagge da cewa babban rashi ne ga al’ummar jihar Kano da na Arewa da ƙasa baki ɗaya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Ibrahim Balarabe Maikaba ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Marigayin a Unguwar Fagge.
Ya yi nuni da cewa a matsayin Marigayin na ‘ya’yansu, kuma abokin aikinsu, mutum ne na ƙwarai mai gaskiya da haƙuri da taimakon al’umma, “Domin shi ne ya taimake su da suka shiga aikin ɗan sanda yana cikin aikin suka zo suka same shi,” in ji shi.
CP Maikaba ya ƙara da cewa, rashin DIG Abdulƙadir Ɗanwawu, babban rashi ne ga al’ummar Fagge, domin jihar Kano ma ta daɗe ba ta sami wanda ya kai matsayin DIG ba sai a lokacinsa. Tun bayan Maye Bashir Wali da ya yi DIG, sai kuma yanzu akwai ɗan asalin Garko DIG Sadiƙ.
Kwamishinan ‘yan sandan na jihar Zamfara ya yi addu’ar Allah ya raya zuriyar marigayi DIG Abdulƙadir Ɗawawu, ya kyautata bayansa, ‘yan’uwansa da mata da su alummar Fagge Allah ya ba su haƙurin juriyar wannan babban rashi.







