Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

Daga Ibrahim Muhammad

Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Dakta Rahila Aliyu Muktar, ta cimma ɗimbin nasarori a cikin shekaru biyu na shugabancinta.

Hukumar ta ƙuduri aniyar samar da rumbun ajiyar jini mallakinta a cikin shekarar 2026, domin amfanin masu buƙatar jini a ƙarƙashin tsarin hukumar, musamman masu larurar amosanin jini, ƙananan yara, mata masu juna biyu, da sauran marasa lafiya masu buƙatar jini.

Dakta Rahila Aliyu Muktar, shugabar Hukumar, ita ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai da ta gudanar, inda ta yi bayani kan nasarorin da Hukumar ta cimma a cikin shekaru biyu na jan ragamar shugabancinta.

Taron ya zo daidai da bikin tunawa da Ranar Lafiya ga Kowa ta Duniya.

Ta ƙara da cewa, Hukumar na da shirin samar da motocin ɗaukar marasa lafiya (ambulances) domin sauƙaƙa jigilar marasa lafiya da ke ƙarƙashin tsarin taimakekeniyar lafiya.

Daga cikin nasarorin da Hukumar ta cimma a ƙarƙashin jagorancinta, Dakta Rahila ta ce sun haɗa da hana salwantar kuɗaɗe da yawansu ya kai Naira miliyan 600 (₦600m), da kuma shigar da rukunin al’umma daban-daban cikin tsarin Hukumar. Waɗannan sun haɗa da mata masu juna biyu sama da mutum dubu 140, ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar sama da dubu 124, masu buƙata ta musamman sama da dubu 46, masu matsananciyar larura sama da dubu 31, masu ɗauke da cutar karya garkuwar jiki sama da dubu 29, da kuma waɗanda ke tsare a gidajen gyaran hali sama da dubu uku.

Dakta Rahila ta yi nuni da cewa, a ƙoƙarin rage tsadar kula da lafiya a tsakanin al’umma, wanda ya haɗa da tsadar magunguna, wahalar zuwa asibiti, da rage mace-macen mata masu juna biyu da yara ƙanana, gwamnatin jihar Kano ta ɗauki muhimman matakai domin tallafa wa waɗannan rukunai.

Ta bayyana cewa, a lokacin da ta karɓi ragamar shugabancin Hukumar, ana kula da mutane sama da dubu 400 ne kacal. Amma sakamakon dabaru da tsare-tsaren aiki da gwamnatin jihar Kano ta ɓullo da su, yanzu adadin ya kusa kai wa mutum dubu 955. Wannan, a cewarta, ya nuna cewa taken wannan shekarar na kula da lafiya ya yi daidai da manufofi da tsare-tsaren Hukumar da na gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Dakta Rahila Aliyu Muktar ta ƙara da cewa, Hukumar na ci gaba da yin haɗin gwiwa da Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, asibitoci, da sauran hukumomi da ke ƙarƙashin ma’aikatar, tare da ƙungiyoyin bunƙasa cigaban al’umma, domin cimma nasarar shirye-shiryenta. Ta kuma yaba da irin goyon baya da gudunmawar da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Yusuf, ke bai wa Hukumar ƙarfin gwiwar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

  • Related Posts

    Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko

    Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne…

    Ibrahim Little Ya Nuna Rashin Amincewa Da Yunƙurin Ganduje nlNa Kafa Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a siyasar jihar Kano, kuma jagoran jam’iyyar ADC a jihar, Alhaji Ibrahim Al-Amin Little, ya bayyana rashin goyon bayansa ga yunƙurin da wasu mutane ke…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Waɗanne Nasarorin Hukumar Taimakekeniyar Kula da Lafiya ta Jihar Kano Ta Cimma?

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Convoluted and Confused Political Situation and Insecurity: A Stop-Gap to State Collapse in History

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Breaking the Chains of Godfatherism: Uba and Fubara’s Path to Autonomous Politics

    Maryam Abacha Accepts Posthumous Doctorate for Late Gen. Abacha, Describes Honour as Well-Deserved