Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jaruman Masana’antar Kannywood, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ƙasa, sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala.
A yayin ziyarar, ƙungiyar ta bayyana Hon. Namadi Dala a matsayin mutum mai kishin cigaban al’umma, wanda ke nuna jajircewa wajen tallafa wa matasa da bunƙasa rayuwarsu.
Haka kuma, sun jaddada goyon bayansu ga dukkan manufofi da shirye-shiryen da ya sanya a gaba domin ci gaban al’umma.
Ƙungiyar Kannywood ta kuma sanar da cewa a babban taronsu na ƙarshen shekara, za su karrama Hon. Namadi Dala domin nuna irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen cigaban al’umma da kuma masana’antar finafinai.
A nasa jawabin, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala ya nuna godiya ga ƙungiyar bisa wannan ziyara ta girmamawa da suka kai masa. Ya kuma ba su shawarwari kan hanyoyin inganta ayyukansu, musamman wajen tabbatar da tsafta, inganci da kyawawan ɗabi’u a harkar shirya finafinai.
A ƙarshe, Hon. Namadi Dala ya bai wa mambobin ƙungiyar Kannywood da suka kai masa ziyara gudunmawa, domin tallafa wa shirye-shiryen babban taron da suke shirin gudanarwa nan gaba kaɗan.





