Daga Ibrahim Muhammad
An buɗe masallacin Juma’a da ƙungiyar Majalisar Matasan Musulmi ta Duniya (WAMY) ta gina a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Ɓaɓura a jihar Jigawa.
Da yake jawabi a wajen taron buɗe masallacin, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibrahim Sabo Birnin Kudu, ya bayyana cewa gina masallaci ga al’umma ba ƙaramin aikin alheri ba ne, yana mai jaddada cewa wannan ne karo na huɗu da ɗalibai suka fara karatu a Jami’ar ba tare da samun masallaci na dindindin ba, ko da na sallolin farilla balle na Juma’a.
Farfesan ya ce yanzu Allah Ya sanya an gina masallacin tare da ƙaddamar da shi, abin da ya ce ya dace a yi wa Allah godiya tare da yaba wa dukkan waɗanda suka ba da gudunmawa wajen tabbatar da wannan aiki na alheri.
Ya ƙara da cewa ba dabara ko wayon Jami’ar ba ne ya haifar da samun masallacin, illa dai haɗin kai da goyon bayan ma’aikata, al’ummar gari da ma gwamnatin jihar Jigawa baki ɗaya, inda ya nuna cewa Hakimin Babura ya taka muhimmiyar rawa wajen zama gada tsakanin jami’ar da ƙungiyar WAMY.
“Abin da ya rage mana shi ne godiya. Muna addu’ar Allah Ya saka wa kowa da alheri,” in ji shi.
Shugaban Jami’ar ya kuma jaddada cewa gina masallaci abu ne guda, amma raya shi da amfani da shi yadda ya kamata shi ne babban abin da ake bukata. Don haka ya yi kira ga kowa da kowa, ba ma’aikatan Jami’ar kaɗai ba, da su ba da gudunmawa wajen tsaftacewa da raya masallacin ta fuskar ibada.
Ya kuma bayyana cewa la’akari da girman Jami’ar da yawan jama’a a lokacin Sallar Juma’a, ana sa ran Jami’ar za ta ƙara gyara harabar masallacin, tare da shirin gina ɓangare na mata domin gudanar da Sallah, da kuma amfani da wani sashe a matsayin makarantar Islamiyya.
A nasa jawabin, wakilin Hakimin Ɓaɓura, Malam Kabiru Abdulrahman, wanda ya kasance cikin masu sa ido kan aikin tun daga farko har zuwa kammalawa, ya yaba wa ƙungiyar WAMY bisa wannan gagarumar gudunmawa, tare da yi mata fatan alheri.
Malam Kabiru ya ce ƙungiyar WAMY ta daɗe tana shahara wajen gina masallatai a wurare daban-daban, tare da taimakon al’umma, musamman talakawa, marayu da marasa lafiya.
Ya ƙara da cewa al’ummar Ɓaɓura, ƙaramar hukuma, jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya suna alfahari da irin ayyukan jinƙai da ƙungiyar WAMY ke gudanarwa domin bunƙasa addinin Musulunci da walwalar al’umma.






