Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa zuwan Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Danmodi, ya zo da sabbin tsare-tsare da matakai na musamman domin farfaɗo da kimar makarantun Kimiyya da Fasaha a faɗin jihar, musamman waɗanda aka gada tun zamanin tsohuwar Jihar Kano, da kuma sababbin makarantun da aka samar domin inganta harkar ilimi.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Jigawa, Farfesa Abbas Jafaru Badakaya, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kano, a lokacin taron tsofaffin ɗaliban Sakandiren Kimiyya na Dawakin Tofa.
Farfesa Badakaya ya ce, a cikin kasafin kuɗin shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin jihar ta ware wa makarantun Kimiyya kuɗaɗe masu yawa da ba a taɓa warewa a tarihin gwamnatocin da suka gabata ba.
Ya ƙara da cewa, a kasafin kuɗin wannan shekara ma, an tanadi kusan Naira biliyan 10 domin bunƙasa makarantun kimiyya da fasaha, abin da ya ce ko rabin hakan ba a taɓa warewa ba tun kafuwar jihar Jigawa.
Ya bayyana wannan a matsayin babbar manuniya ta kyakkyawar niyya da jajircewar gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Malam Umar Namadi wajen farfaɗo da martaba da inganta makarantun Kimiyya da Fasaha, lamarin da ke da gagarumin tasiri ga bunƙasar ilimi a jihar.
Babban Sakataren ya ƙara da cewa, sakamakon irin wannan kulawa da gwamnati ke bai wa fannin ilimi, ana aiwatar da ayyuka daban-daban a makarantun Kimiyya da Fasaha; wasu ayyukan an riga an kammala su, wasu kuma na ci gaba da gudana, yayin da aka tanadi wasu ayyuka a cikin kasafin kuɗin sabuwar shekarar da ke tafe.
A ƙarshe, Farfesa Abbas Jafaru Badakaya ya yi kira ga tsofaffin ɗalibai da su yi koyi da ‘yan aji na shekarar 1984 na Dawakin Tofa, ta hanyar kula da malamansu, ko waɗanda suka rasu ko kuma waɗanda suke raye, ta kowace hanya da za ta taimaka wajen kyautata rayuwarsu da kuma girmama gudunmawar da suka bayar a fannin ilimi.






