Kungiyar KASSOSA ta Dawakin Tofa (Aji na 1984) Ta Shirya Taron Tunawa da Marigayi Malam Haruna Ungogo

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Sakandiren Kimiyya ta Dawakin Tofa, aji na 1984, ƙarƙashin ƙungiyar KASSOSA, ta gudanar da wani taron jawabai na musamman domin tunawa da marigayi Ambasada Malam Haruna Ungogo, bisa gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkar ilimi a rayuwarsa.

An gudanar da taron ne a birnin Kano, inda manyan baƙi da dama suka halarta.

Daga cikin su akwai Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa, Alhaji Bashir Ɗalhatu, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar Jigawa.

A jawabinsa, Alhaji Bashir Ɗalhatu ya bayyana muhimmancin rawar da malamai ke takawa wajen gina al’umma, tare da yaba wa tsofaffin ɗaliban bisa shirya irin wannan taro na zumunci da tunawa da gudunmawar malamansu.

Ya kuma yi kira ga tsofaffin ɗalibai da su ƙara ƙaimi wajen tallafa wa ilimin yara, musamman waɗanda ba sa zuwa makaranta.

A cewarsa, wani bincike na duniya ya nuna cewa akwai kusan yara miliyan 18 a Nijeriya da ba sa zuwa makaranta, inda miliyan 15 daga cikinsu ke yankin Arewa. Don haka, ya jaddada buƙatar tsofaffin ɗalibai su taka rawar gani wajen rage wannan matsala.

Haka zalika, wakilin Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tsohon Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano kuma Babban Darakta a Hukumar Kula da Kananan Hukumomi, Farfesa Ibrahim Jibrin, ya isar da saƙon fatan alheri daga Gwamnan Kano ga mahalarta taron.

Ya kuma bayyana kyawawan halaye da jajircewar marigayi Malam Haruna Ungogo, inda ya ce sun taɓa yin aikin koyarwa tare, kuma ya san shi a matsayin malami nagari mai kishin ilimi.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Sakandiren Kimiyya ta Dawakin Tofa, aji na 1984, Alhaji Garba Ibrahim El-Sulaiman, ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatoci ke yi wajen bunƙasa ilimi, musamman ta hanyar ware kuɗaɗe masu yawa domin inganta harkar ilimi.

Shugaban Kwamitin Shirya Taron kuma Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Aji na 1984, Dakta Sulaiman Muhammad, ya nuna farin cikinsa da irin halartar da taron ya samu.

Ya ce dalilin shirya taron shi ne tunawa da marigayi Malam Haruna Ungogo da kuma irin tasirin da ya yi a rayuwarsu, inda ya ce duk matsayen da suka kai a yau, malaminsu ne ya sa su a kan turba madaidaiciya.

Dakta Sulaiman ya bayyana marigayin a matsayin malami jajirtacce, mai son cigaban ɗalibansa da abokan aikinsa, wanda a kullum yake fatan ganin kowa cikin walwala da hazaƙa wajen karatu da koyarwa.

Ya ƙara da cewa za su riƙa shirya irin wannan taro na tunawa da shi duk bayan shekaru biyu, tare da gayyato masana daban-daban domin gabatar da jawabai a kansa.

Haka kuma, ya yaba da irin kulawar da gwamnatin jihar Kano ke bai wa harkar ilimi ta hanyar ware kasafi mai tsoka, tare da fatan gwamnati za ta ƙara himma a wannan fanni.

Ya bayyana cewa mutane 14 ne aka karrama a taron, ciki har da marigayi Malam Haruna Ungogo, da malamai masu rai da kuma waɗanda suka rasu.

Ya kuma yaba da goyon bayan da ƙungiyar KASSOSA ke bai wa shirye-shiryensu.

A nasa jawabin, Farfesa Abbas Ja’afaru Badakaya, Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Jigawa, ya bayyana taron a matsayin na tunawa da mutum mai matuƙar tasiri a rayuwar tsofaffin ɗalibai, inda ya ce marigayi Malam Haruna Ungogo ya cancanci irin wannan girmamawa.

A ƙarshe, Farfesa Abdulkadir Sarki Abba, tsohon ɗalibin Sakandiren Kimiyya ta Dawakin Tofa (Aji na 1984) kuma mazaunin Amurka, ya gabatar da jawabi na musamman kan halaye, ɗabi’u da kuma gagarumar gudunmawar da marigayi Malam Haruna Ungogo ya bayar ga rayuwar ɗalibansa.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum