Daga Khalid Idris Doya
A ranar Talata mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya jagoranci tawagar Majalisar dattawa domin miƙa ta’aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bayan gabatar da ƙuduri na musamman a zauren Majalisar domin karrama Shaikh Dahiru da yaba wa irin gudunmawar da ya bayar a lokacin da ya ke raye.
Kazalika, shi ma Kakakin Majalisar Wakilai na tarayya Hon. Tajudden Abbas ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar wakilai a wajen ta’aziyyar wanda ya gudana a Masallacin marigayin da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi. Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Auwal Jatau ne ya amshi tawagar.
Da su ke miƙa ta’aziyyar, Sanata Barau ya bayyana cewar rasuwar Sheikh Dahiru babban rashi ne da Nijeriya da ma Afrika suka yi, ya ce dukkanninsu sun ji matuƙar zafin rashin babban Malamin wanda ya zama uba, jagora kuma hadimin addinin Musulunci.
Ya ce a zaman majalisar na ranar Talata ta gabatar da wani ƙudiri na musamman wanda dukkanin sanatoci suka yi alhini da juyayin rasuwar Shaikh Dahiru Usman Bauchi, “Dukkanin Sanatoci ba kawai zallar musulmai ba har da Kiristocin cikinmu kowa ya nuna irin babban rashin da aka yi, da jinjina masa kan hidimar da yayin wa addinin musulunci da bayar da gudummawarsa wajen kyautata zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan.”
“Mun zo ne a madadin majalisar dattawa a bisa ƙudirin musamman da aka gabatar, don haka muna jajanta wa gwamnatin jihar Bauchi, iyalai, al’ummar jihar da Musulmai baki ɗaya.”
Ya ce rashin Shaikh Dahiru rashi ne da duniya ta yi, “Ayyukan da Shaikh Dahiru ya yi sun wuce Nijeriya, sun wuce maganar Afrika, yana daga cikin malaman da ake ji da su a duniya baki ɗaya.”
Barau ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa ya gafarta masa. Sannan ya nemi iyalansa da su ya ƙoƙarin koyi da kyawawan ɗabi’u na mahaifinsu.
Tawagar majalisar dattijai ta haɗa da Sanata Sani Musa, shugaban kwamitin kuɗi; Sanata Muttati Dan Dutse, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da manyan makarantu; Sanata Shehu Buba Umar, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kiwo; Sanata Abdul’aziz Yar’adua, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji; da hamshaƙin ɗan kasuwar mai Jack Rich, shi ma ya shiga tawagar majalisar dattawa.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan magayin, Dr. Bashir Dahiru Bauchi, ya gode wa tawagar Majalisar Dattawan bisa ziyarar da jajantawa.
A ɓangaren kakakin majalisar wakilai kuwa, Hon. Tajudden Abbas ya ce sun zo ne domin su wakilci dukkanin ‘yan majalisun tarayya su 360 domin miƙa ta’aziyyarsu bisa wannan babban rashin da Nijeriya ta yi.
“Wannan rashin ba rashi ne na mutanen Bauchi ba, ba rashi ne na Nijeriya ba, kima da ɗaukaka na Malam Dahiru ya zama na duniya ba ma Afrika ko Nijeriya ba; duk wani malami mai amsa sunan malamanta ya san ɗaukaka da irin rayuwa da babbanmu, kakanmu Malam Dahiru ya yi a tsawon rayuwarsa na hidima wa addini a wannan ƙasar.”
Ya ce yawan ɗalibai da Shaikh ɗin ya koyar sun ce a ce Nijeriya ne kaɗai don haka ya ce rashin ke na duniya. Sun miƙa ta’aziyyarsu wa gwamnatin Bauchi, Sarkin Bauchi, iyalai da ma jama’a Bauchi.
Daga cikin tawagar Majalisar wakilai akwai shugaban mai tsawatarwa na majalisar, Hon. Usman Bello Kumo; shugaban kwamitin kasafi, Hon. Abubakar Kabir Bichi; shugaban kwamitin harkokin mai, Hon. Alhassan Ado Doguwa; mataimakin shugaban marasa rinjaye, Aliyu Sani Madaki; shugaban kwamitin kula da harkokin tashoshin ruwa, Hon. Nnolim Nnaji da dai sauransu.
Sai kuma ‘yan majalisar tarayya daga Bauchi kamar su Bappa Aliyu Misau, Ali Garu da dai sauransu.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin Alhaji Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi ne ya yi jawabin godiya a madadin iyalai, inda ya ce wa ‘yan majalisun dokokin wannan rashin gaba daya ne aka yi, don haka ya ce sun gode da ziyarar.
Wakilinmu ya labarto cewa ana ta kan ci gaba da amsar ta’aziyyar rasuwar malamin wanda ya rasu a ranar Alhamis. Tawagar daga sassan Nijeriya da ma ƙasashen Afrika ne ke ta zuwa domin mika ta’aziyyarsu.






