Gwamnatin Jigawa Na Ƙarfafa Ilimin Addinin Musulunci -Ado Maje Sale

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnatin jihar Jigawa na ci gaba da ɗaukar matakai domin bunƙasa ilimin addinin Musulunci, musamman ta hanyar tallafa wa yara da matasa masu hazaƙa a fannin karatun Alƙur’ani da harshen Larabci.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Jigawa shawara a ɓangaren ilimin matakin farko, Hon. Ado Maje Sale (mai ritaya), ne ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Harshen Larabci ta Duniya da Ƙungiyar Raya Al’adu da Harshen Larabci ta Karamar Hukumar Birnin Kudu ta shirya a ranar Alhamis.

Hon. Ado Maje Sale ya bayyana Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, a matsayin shugaba mai kishin ilimin addini, inda ya ce yana ba da kulawa ta musamman ga duk wani shiri da ya shafi bunƙasa addinin Musulunci a faɗin jihar.

Ya ce Gwamnatin Jihar na goyon bayan dukkanin gasar musabaƙa da ake gudanarwa, wanda hakan ke bai wa jihar damar samun nasarori a matakin ƙasa da ma wakilci a manyan musaɓaka na duniya.

A cewarsa, a halin yanzu akwai sama da yara bakwai da suka wakilci jihar Jigawa a gasar musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa, inda wasu daga cikinsu Gwamnan Jihar ya ɗauki nauyin karatunsu na digiri da digiri na biyu a jami’o’in ƙasashen waje sakamakon bajintar da suka nuna.

Hon. Ado Maje Sale ya bayyana taron bikin Ranar Harshen Larabci ta Duniya da aka gudanar a Birnin Kudu a matsayin abin alfahari, yana mai cewa taron ya ƙara ɗaukaka darajar addini da martabar karamar hukumar da ma jihar baki ɗaya.

Ya kuma bayyana cewa, duk da rashin halartar Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Dakta Muhammad Uba, sakamakon rashin kasancewa a gari, ƙaramar hukumar na bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasa rayuwar al’umma, tare da shirin ƙara tallafa wa ƙungiyar ta hanyar samar da ofis da kuma faɗaɗa ayyukanta zuwa birane da ƙauyuka.

Hon. Ado Maje Sale ya nuna damuwa kan yadda wasu ’yan siyasa da attajiran ’yan kasuwa ke yin sakaci wajen halartar tarukan da suka shafi ilimin addini, inda ya ce irin waɗannan taruka na da matuƙar muhimmanci wajen gina al’umma.

Ya yi kira ga ’yan siyasa da ’yan kasuwa a Birnin Kudu da su riƙa bayar da gudunmawa domin ƙarfafa gwiwar yara da matasa masu tasowa a fannin addini.

A nasa jawabin, Sakataren Ƙungiyar Ɗaliban Larabci ta Birnin Kudu, Malam Adamu Yakub Saleh, ya ce ƙungiyar na fuskantar matsaloli da suka shafi ƙarancin kayan aiki a makarantar Larabci, ciki har da rashin ɗakin karatu, ofishin gudanarwa da kuma katanga, duk da yawan ɗaliban da ke karatu a makarantar.

Shi ma Hon. Salisu Muhammad, mai bai wa Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu shawara kan harkokin al’adu da walwala, ya ce taron ya nuna akwai yara masu hazaƙa a yankin, inda ya jaddada buƙatar samun tallafi domin bai wa irin waɗannan yara damar bunƙasa baiwar da Allah Ya ba su.

  • Related Posts

    Iyaye da Gwamnati Su Ƙara Ba da Kulawa Ga Makarantun Alƙur’ani – Malam Mahmud TijjaniUsman Zangon Barebari

    Malam Mahmud Tijjani Usman Zangon Barebari ya yi kira ga iyaye da kuma gwamnati da su riƙa ba da kulawa ta musamman ga makarantun Alƙur’ani, domin inganta tarbiyyar yara da…

    Jami’ar Kebbi Ta Karrama Gwamna Lawal da Digirin Girmamawa

    Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero a Jihar Kebbi ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da digirin girmamawa na Dakta na Kimiyya (D.Sc Honoris Causa),…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta