Malam Mahmud Tijjani Usman Zangon Barebari ya yi kira ga iyaye da kuma gwamnati da su riƙa ba da kulawa ta musamman ga makarantun Alƙur’ani, domin inganta tarbiyyar yara da tabbatar da makomarsu a duniya da lahira.
Malam Zangon Barebari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen walimar yaye mahaddatan Alƙur’ani da makarantar Madinatul Ahbab Daiba ta shirya a harabar Masallacin Shehu Ahmadu Tijjani, da ke Ƙofar Mata, a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa taron saukar Alƙur’ani taro ne na farin ciki da albarka, kasancewar Manzon Allah (SAW) ya umarci al’umma da su tarbiyyantar da ‘ya’yansu a kan abubuwa uku: karatun Alƙur’ani, son Manzon Allah (SAW), da kuma son Ahlul Baiti.
Malam Zangon Barebari ya ce ganin yadda yara sama da 100 suka haddace Alƙur’ani a wannan makaranta abin farin ciki ne matuƙa, inda ya ƙara da cewa malamai sun bayyana karantar da yara Alƙur’ani a matsayin abin da ke kwantar da fushin Ubangiji.
Ya ce a wannan zamani ya zama wajibi a ƙara ba da muhimmanci ga karatun Alƙur’ani tare da ƙarfafa shi.
Ya yaba da makarantar Madinatul Ahbab Daiba ƙarƙashin jagorancin Shehu Malam Dan Almajiri, inda ya ce makaranta ce mai asali da albarka, wadda ba kasafai ake samun irinta ba, face dai a yi koyi da tsarin tafiyarta.
Ya kuma bayyana taron saukar Alƙur’ani a matsayin abin farin ciki da alfahari.
Malam Zangon Barebari ya yi kira ga iyaye da su ƙara zage dantse wajen tallafa wa yaransu domin su riƙa zuwa makarantun Alƙur’ani, tare da yin hidima ga malamai masu karantar da su.
Ya nuna damuwa da yadda wasu iyaye ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tura yara makarantun zamani, amma su kasa ba da irin wannan kulawar ga makarantun Alƙur’ani.
Ya bayyana hakan a matsayin babban ƙalubale ga iyaye, inda ya buƙace su da babbar murya da su dage wajen tallafawa malamai masu koyar da Alƙur’ani, domin wannan ilimi shi ne zai amfani yaro a duniya da lahira.
Ya ƙara da cewa ilimin zamani ana nema ne domin duniya, wanda a ko’ina za a iya samun sa, amma ilimin Alƙur’ani sai da ƙoƙari da sadaukarwa.
Haka zalika, Malam Zangon Barebari ya yi kira ga gwamnati da ta ƙarfafa makarantun Alƙur’ani ta hanyar ba su tallafi da kulawa ta musamman, yana mai cewa zaman lafiyar al’umma ma yana da alaƙa da irin waɗannan makarantu, domin suna taimakawa wajen kwantar da fushin Ubangiji.
Ya ce idan Allah Ya yarda da al’umma, to ko hukumomi za su zauna lafiya.
A ƙarshe, ya ja hankalin ɗaliban da suka haddace Alƙur’ani da su sani cewa yanzu ne farkon tafiyarsu, ba ƙarshenta ba.
Ya ce haddace Alƙur’ani kamar samun maɓuɗin alheri ne; muddin mutum ya riƙe shi, ba zai ɓace ba, kuma zai buɗe masa ƙofofin alheri a duk inda ya dosa.
Ya ƙara da cewa idan mutum ya yi sakaci har Alƙur’ani ya subuce masa, to kamar ya yar da maɓuɗinsa ne, wanda hakan kan jefa shi cikin wahala. “Amma wanda ya kiyaye Alƙur’ani, yana da tabbacin samun sauƙi da buɗaɗɗen alheri a dukkan lamuransa, da yardar Allah,” ya ƙarƙare.








