Daga Ibrahim Muhammad
Mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara ta musamman kan harkokin Majalisar Dokoki, Rt. Hon. Isyaku Ali Ɗanja, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf na tafiya lafiya da Majalisar Dokokin jihar Kano, ba tare da wani rikici ko rashin fahimta ba.
Isyaku Ali Ɗanja ya ce a tsawon wannan gwamnati ba a taɓa samun wata matsala ko hayaniya tsakanin Gwamna da Majalisar Dokokin jihar Kano ba, lamarin da ke nuna kyakkyawar fahimta da mutunta juna a ɓangarorin biyu.
Ya bayyana cewa hakan ya samo asali ne sakamakon yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ke sauke haƙƙoƙin kowane ɓangare yadda ya kamata. “Da a ce ana tauye haƙƙoƙin ’yan majalisa, da tuni an ji koke-koke ko hayaniya,” in ji shi.
Ɗanja, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, tare da wakiltar ƙaramar hukumar Gazawa, ya ce Majalisar ba baƙuwa ba ce a gare shi, kasancewar ya shafe tsawon shekaru 16 yana aiki a cikinta, inda ya riƙe muƙamai daban-daban da suka haɗa da Shugaban Masu Rinjaye, Mataimakin Shugaban Majalisa, har zuwa Kakaki.
Ya ƙara da cewa a matsayinsa na mai ba Gwamna shawara, yana yin iya ƙoƙarinsa wajen tabbatar da an samu zaman lafiya da fahimta tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa domin ciyar da jihar gaba.
Da yake jawabi kan biyan kuɗaɗen tsofaffin kansiloli, Ɗanja ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cika alƙawarin da ya ɗauka na biyan tsofaffin kansilolin Gwamna Abdullahi Ganduje da ba a biya su a baya ba. Ya ce hakan ya nuna tausayi, sanin ya kamata da kuma kishin sauke nauyin da ke kansa, abin da ya sa tsofaffin kansilolin ke masa addu’a da fatan Allah Ya saka masa da alheri.








