Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kan hanyar samun ƙarin manyan nasarori a babban zaɓen shekarar 2027, bisa yadda zabubbukan cikin gida na jam’iyyar suka gudana cikin nasara da haɗin kai.
Hon. Ibrahim Namadi Dala, wanda ya jagoranci gudanar da zaɓen shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar, ne ya bayyana hakan a Kano, inda ya ce sakamakon zaɓen ya nuna ƙarfafa gwiwa da ƙaruwar karɓuwar NNPP a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya taya dukkan waɗanda aka zaɓa, tun daga matakin mazaɓu har zuwa matakin ƙasa, murna, tare da yi musu fatan alheri da kuma kira gare su da su sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya dace, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a kowane mataki.
Hon. Namadi Dala ya ƙara da cewa nasarar zaɓen ta bayyana ƙarfin haɗin kai, jajircewa da ƙwazon magoya bayan NNPP a shiyyar Arewa maso Yamma, lamarin da ke nuna kyakkyawar makomar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano ya kuma bayyana godiyarsa ga jagoran jam’iyyar, Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa kyakkyawan jagoranci da goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar a kowane lokaci.
Haka kuma, ya yaba da jajircewa da biyayyar da magoya bayan NNPP ke nunawa a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa hakan ne ginshiƙin samun nasarorin da jam’iyyar ke samu a halin yanzu da kuma waɗanda ake sa ran samu a nan gaba.






