Daga Ibrahim Muhammad Kano
Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawaa jihar Kano, Hon. MB Aliyu, ya bayyana cewa kujerar da yake riƙe da ita a Majalisar Jiha amana ce, ba ta sayarwa ba, yana mai jaddada cikakkiyar biyayyarsu ga jagoran Kwankwasiyya, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Hon. Aliyu ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai, bayan al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa sun kai ziyara ga jagoran Kwankwasiyya domin jaddada goyon bayansu da biyayya ga tafiyar.
Ya ce tsarin Kwankwasiyya tun asali tsarin amana ne, inda duk wanda ya shiga dole ne ya zama mai riƙe da amana. “Kowa ya san yadda aka shigo wannan tsari, don haka ba abin mamaki ba ne a ce Kwankwasiyya na riƙe da amana,” in ji shi.
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa al’ummar Nasarawa daga mazañu 11, tare da shugabanninsu, sun yi mubaya’a ga jagoran Kwankwasiyya, tare da tabbatar masa da cikakken goyon baya ga tafiyar da yake jagoranta.
Hon. MB Aliyu ya jaddada cewa za su ci gaba da biyayya ga tsarin Kwankwasiyya har illa masha Allah, yana mai cewa ko da jagora ya buƙaci a bar kujerarsa, hakan ba zai girgiza imaninsu ba.
“Mun san duk wanda ya bi Kwankwaso ba zai yi da-na-sani ba,” in ji shi.
Ya tunatar da irin abubuwan da suka faru a baya, inda ya ce Kwankwasiyya ta fara ba tare da wata kujera ba, amma daga bisani ta kafa gwamnati tare da samun ‘yan majalisa da shugabannin ƙananan hukumomi.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda wasu da aka tsayar aka zaɓa suka yi butulci ga tsarin.
Ɗan majalisar ya kuma yi zargin cewa ana ciniki da muƙamai a wasu ƙananan hukumomi, inda ya ce ana biyan wasu ‘yan majalisu da shugabanni kuɗaɗe domin sauya matsaya.
“A nan nake ƙara tabbatarwa cewa kujerar ƙaramar hukumar Nasarawa a Majalisar jiha ba ta da farashi. Amana ce da aka ɗora mana, kuma za mu ci gaba da riƙe ta,” in ji Hon. MB Aliyu.
Ya ce akwai wasu abubuwa da ke a ɓoye da nan gaba za su fito fili, yana mai nuni da cewa lamarin butulcin da ake gani ba abu ne mai sauƙin fahimta ba, musamman idan aka yi la’akari da tarihin wasu shugabanni a jihar.
A karshe, Hon. MB Aliyu ya gode wa jagoran Kwankwasiyya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa jagoranci da ya ba su dama suka shiga siyasa.
Ya jaddada cewa al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa ba su da farashi, haka nan jagoransu ma ba abin saye ba ne.






