Daga Ibrahim Muhammad Kano
Jagoran Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Nasarawa, Kano, Alhaji Mustapha Muhammad Mai Sikeli, ya bayyana jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mutum mai haƙuri da natsuwa, wanda ba ya furta magana sai ya yi nazari kan abin da ka iya faruwa nan gaba.
Mai Sikeli ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar ‘yan Kwankwasiyya daga ƙaramar hukumar Nasarawa a wata ziyara da suka kai wa Dakta Kwankwaso a gidansa da ke titin Mila, domin jaddada goyon bayansu da biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya.
Ya ce su da suka yi zamani da marigayi Malam Aminu Kano sun fahimci cewa Kwankwaso na tafiya ne a irin wannan tafarki, yana mai cewa a halin yanzu babu wani ɗan siyasa a faɗin ƙasar nan da ya kai shi kishin jama’a da taimakon marasa ƙarfi.
Alhaji Mustapha Mai Sikeli ya ƙara da cewa hakan bai ba su mamaki ba, domin duk wanda ya yi biyayya ga iyayensa, ya girmama mahaifi da mahaifiya, Allah kan hore masa jama’a. “Wannan ne abin da muke gani a rayuwar jagoran Kwankwasiyya,” in ji shi.
Ya bayar da misali da gaskiyar Kwankwaso, inda ya ce a lokacin da yake cikin Hukumar mai ta ƙasa (NNPC) a zamanin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, ya nemi a cire shi daga cikin mambobin Hukumar sakamakon rashin gaskiyar da yake gani, daga bisani kuma aka tura shi aikin jakadanci.
Mai Sikeli ya ce Kwankwaso mutum ne mai sauƙin kai, wanda ba shi da girman kai, yana girmama masoyansa, tare da nuna kulawa ga kowa. “A duk faɗin Nijeriya, babu wani babban ɗan siyasa da ke da masoya da mabiyan gaskiya irin nasa,” in ji shi.
Ya ce duk da cewa sun taimaka wajen kafa gwamnati, shi kansa bai taɓa cin gajiyar wani abu ba daga cikinta. Ya ce su kan je wajen jagora suna roƙon ya kare gwamnatin Abba Kabir Yusuf, amma abin mamaki a cewarsa, sai aka fuskanci butulci. “Ta yaya za mu bi wanda ya yi butulci ga tafiyar?” in ji shi.
Mai Sikeli ya ƙara da cewa jagora ya yi musu jawabi inda ya bayyana cewa duk wanda yake jin bai gamsu ba, yana da ‘yancin bin duk inda ransa ya so, amma tafiyar Kwankwasiyya za ta shiga wani sabon tsari.
Ya ce ko da sun shafe shekaru takwas ba tare da mulki ba, ba za su damu da shekara guda ba.
Ya jaddada cewa ‘yan Kwankwasiyya na da ƙarfin tushe a ƙasa, inda ya ce ko yau aka ce kowa ya koma mazaɓarsa a ƙananan hukumomi 44 a gudanar da zaɓe, kafin magariba Kwankwasiyya za ta yi nasara.
Alhaji Mustapha Mai Sikeli ya kuma bayyana cewa sun ji kalaman Allah-wadai daga wasu mata kan abin da ya faru, yana mai cewa wasu na ganin an ci amanar lokacin da suka sadaukar domin ganin tafiyar ta yi nasara.
A ƙarshe, Mai Sikeli ya ce su a ƙaramar hukumar Nasarawa sun yi shawara da tuntuɓa a matakai daban-daban, inda suka tabbatar da biyayya ga jagoran Kwankwasiyya ba tare da sharadin neman mukamai ba.
Ya yi kira ga ‘yan Kwankwasiyya a Nasarawa da ma faɗin jihar Kano da su kwantar da hankalinsu, su guji tsokana, amma ya gargaɗi cewa idan aka tsokane su, za a ji martaninsu.








