Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir ya yi kira ga ‘yan siyasa, musamman a jihar Kano, da su riƙa sanya mutumci, ilimi, hangen nesa da sanin ya kamata a harkar adawar siyasa, maimakon rikice-rikice da cin mutunci da ake gani a wasu lokuta.
Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir, wanda shi ne Hadimi na Musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasa, Sanata Barau I. Jibrin, kan harkokin kasuwanni (Waya), ya yi kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya bayyana cewa duk da kasancewar siyasa tana ɗauke da adawa, akwai buƙatar a riƙa gudanar da ita cikin mutuntawa, ilimi, cancanta da sanin ya kamata.
Ya ƙara da cewa Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya umarci bayinsa da yin gasa wajen neman rahama da gafararsa, inda ya ce ayyukan alheri sune abin da ya kamata a yi takara a kai, har ma da a fagen siyasa.
Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir ya ce a dukkan harkokin rayuwa -ko na kasuwanci, ko na aiki, ko na siyasa- ya kamata mutum ya yi abubuwan da za su zame masa sanadin samun yardar Allah da shiga Aljanna, ba wai abin da zai jawo masa laifi ko nadama ba.
Ya yi gargaɗi da cewa yin adawar siyasa ba tare da iyaka ba na iya kai wa ga cin mutuncin mutane, lamarin da ka iya zama sanadin hukunci a wurin Allah, ko kuma sakamako tun a wannan duniya.
Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir ya kawo misali da Hadisin Manzon Allah (SAW) da ya tambayi Sahabbai ko sun san wane ne matsiyaci. Sahabbai suka amsa cewa matsiyaci shi ne wanda ba shi da dukiya. Sai Manzon Allah (SAW) ya bayyana musu cewa matsiyaci na gaskiya shi ne wanda zai zo ranar Alƙiyama da Sallah, Azumi, Zakka da ayyukan alheri masu yawa, amma saboda ya zagi mutane, ya doke wasu, ya ƙwace dukiyar wasu, za a ɗauki ayyukansa na alheri a raba wa waɗanda ya zalunta, har sai sun ƙare, sannan a ɗora masa zunubansu, a jefa shi wuta.
Ya ƙara da cewa ko tun a duniya ma, mutum na iya fuskantar hukunci idan ya ci mutuncin mutane, inda ya ce an riga an ɗaure mutane da dama bisa laifin cin zarafi da bata suna.
Ya kafa misali da yanayin siyasar jihar Kano a yanzu, inda wasu ‘yan siyasa suka yi maganganu marasa daɗi kan Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sakamakon adawar siyasa.
Ya ce idan har wani sauyi ya faru nan gaba, to irin waɗannan maganganu za su iya zama abin kunya ga masu su, domin kunya wani ɓangare ne na imani.
Saboda haka, Ambasada Ibrahim Rabi’u Tahir, Hadimi na Musamman ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasa, Sanata Barau I. Jibrin, kan harkokin kasuwanni, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su gyara irin waɗannan munanan ɗabi’u, tare da fahimtar cewa siyasa ana yin ta ne domin samar da ci gaba da bunƙasa al’umma.
Ya ce ya zama wajibi ‘yan siyasa su haɗa kai domin ciyar da jihar Kano gaba, su koyi darasi daga irin cigaban da wasu jihohi kamar Legas suka samu, maimakon amfani da adawa a matsayin hanyar cin mutunci ko haddasa rikici.






