Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana ƙaramar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano da cewa suna zaune lafiya babu rigimar siyasa ko wani abu na daban a tsakanin ‘yan Kwankwasiyya, jagorancinsu da shugabancin su da masu muƙamai na siyasa, kowa yana yin abin da ya dace.
Injiniya Iliyasu Usman ɗan kasuwa kuma jigo a jam’iyyar NNPP daga ƙaramar hukumar Nasarawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Kwankwaso yayin ɗaurin auren ‘ya’yan mai bai wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf shawara a kan siyasa Sanusi Surajo Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa su al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa ginshiƙin ne a siyasar jihar Kano, duk wani abu da za a gani a ƙananan hukumomi 44 yawanci daga gare su ake kwafa, ko jagoran Kwankwasiyya yana yawan cewa a nemi ‘yan Nasarawa in wani abu ya taso domin su a tafiyar Kwankwasiyya suna kan gaba, duk abin da za a yi suna yi da kyakkyawan aƙida, manufa da jajircewa a kan bin umurnin Jagora.
Injiniya Iliyasu Usman ya ce tafiyar gwamnatinsu ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf tana tafiya yadda ya kamata abubuwa da ake tarihi ne yake maimaita kansa abubuwa da Gwamna yake na ayyuka sai a yi masa fatan alkhairi da addu’a wannan nasarori da ya sako a gaba yake samu Allah ya ida su ya sa a dace.
Ya ce mutanen Kano sune shaida yadda gwamnatin da ta shuɗe suka yi shekara takwas ba abin da ake ban da sace-sace da fashe-fashe, yanzu kuwa duk wanda ya shigo Kano ya san ai an sami sauƙi, mutanen jihar Kano ƙananan hukumomi 44 da maƙwabtanta sune ya kamata a ji bakunansu na faɗin alkharin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa a gari.
Injiniya Iliyasu Usman ya musanta zargin da ake yi na cewa jagoran Kwankwasiyya zai koma jam’iyyar APC, domin tafiyar Kwankwaso kamar ruhi ce, ita kanta APC idan ta tsinci kanta a tsarin Kwankwasiyya ai ta narke, maganar ma a ce zai koma APC, to shi yake neman su ma ke nan, amincin jama’ar Kano ake nema, kuma sun amince da wannan tsarin.
Ya ce duk wanda yake ganin jagora Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai koma wani waje daga inda yake, to mai wanann tunanin ko dai lissafinsa makahon lissafi ne, ko kuma yana da naƙasu a tafiyar da ake yi.
Injiniya Iliyasu Usman ya ce, “Irin wannan tasiri da amincewa da al’umma suka yi da tsarin siyasar Kwankwaso saboda shi mutum ne mai aminci da amana, kuma ba a taɓa ba shi amana ya ci ba, yanzu a Kano su waye ma ‘yan adawar su da suke cewa ‘yan adawa ne, sun ma kasa riƙe kawunansu da kula da abubuwa da ya kamata su yi, rigima ake. A’a wannan Barau ne. Wannan Ganduje ne. Wannan waye kaza. Gwamnan Kano ake so da tsarin Kwankwasiyya su yi haƙuri su dawo da wasu abubuwa.”
Ya ce, “Ashe ba za su iya ba ke nan? Jiya ma mai ta yi balle yau? Mutanen Kano sun sani, in ka ɗauki tsarukan da gwamnatin Kwankwasiyya ta zo da shi ƙarƙashin fasihin Gwamna in ana maganar cigaba, in dai mutum ba wanda ya rasa hankali ba ne, waye zai zaɓi APC? Me ake yi a cikinta? Rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ko salwantar rayukan al’umma ko fatara ko haraji da ake so a ƙaƙaba wa mutane su cigaba da wahala.
Injiniya Iliyasu Usman ya ce duk abin da mutane za su je su zaɓa su dai sunanan a tsarin Kwankwasiyya, kuma ita za su yi kuma da yardar Allah ita ce har abada a Kano.








