Daga Ibrahim Muhammad Kano
An gudanar da bikin cikar Dagacin Gama, Alhaji Rabi’u Isyaku, shekaru 25 kan karagar mulki, a fadarsa da ke garin Gama, ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, a ranar Lahadi.
Da yake jawabi a wajen taron, Dagacin Gama ya bayyana godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba shi damar cika shekaru 25 tun daga lokacin da aka naɗa shi Dagaci.
Ya ce wannan lokaci ya kasance mai albarka da cike da tarihi a rayuwarsa da kuma Masarautar Gama gaba ɗaya.
Alhaji Rabi’u Isyaku ya nuna farin cikinsa da yadda ake zaman lafiya a yankin duk da kasancewar al’umma masu bambancin ƙabilu, addinai da harsuna. Ya jaddada cewa tun hawansa mulki bai taɓa samun saɓani da kowa ba, sakamakon kyakkyawar hulɗa da shugabanni tun daga Masarautar Kano, hakimai, masu unguwanni, wakilai da kuma gwamnatoci na baya da na yanzu a matakan ƙaramar hukuma da jiha.
Dagacin ya yaba da rawar da masu unguwanni, malamai da sauran masu ba shi shawarwari ke takawa wajen sauke nauyin jagoranci.
Haka kuma, ya gode wa ƙungiyar Gama ƙarƙashin jagorancin Farfesa Muhammad Shehu Husaini, da kuma dukkan masu bayar da gudunmawa ga ci gaban garin.
Ya kuma yaba da jajircewar jami’an ’yan sanda na Gwagwarwa da ke kula da tsaron yankin tun hawansa mulki.

Ya ce ba zai manta da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ba, domin a zamansa ne aka naɗa shi Dagacin Gama. Ya bayyana cewa ya yi zamani da sarakuna uku, inda a halin yanzu yake mulki a zamanin Khalifa Muhammad Sanusi II, wanda yake nuna masa cikakkiyar biyayya tare da isar da dukkan umarnin da ke fitowa daga Masarautar Kano da ofishin hakimi ga al’umma.
Dagacin Gama ya kuma gode wa hakimai, wakilai da masu unguwanni, da waɗanda suke raye da kuma waɗanda suka rasu, bisa irin gudunmawar da suka bayar tun daga nadinsa.
Ya roƙi gafarar duk wanda ya taɓa yi wa kuskure ba da gangan ba, tare da bayyana cewa ya yafewa kowa.
A nasa jawabin, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. MB Aliyu, ya ce Allah Ya albarkaci Gama da al’umma iri-iri daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya bayyana cewa garin na da manyan ’yan siyasa, ’yan kasuwa, manyan ma’aikatan gwamnati, mahaddatan Alƙur’ani da limamai, inda ya ce komai ya haɗu a Gama, abin da ya dace a yi shi ne godiya ga Allah.
Hon. MB Aliyu ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Dagacin Gama lafiya da tsawon rai, tare da albarkantar da dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen gudanar da bikin.
Ya ce a matsayinsu na ’yan asalin Gama, sun ɗauki alƙawarin ci gaba da tallafa wa masarautar, inda ya nuna farin ciki da yadda aka gina masarautar Gama bisa tsari, ta yadda duk wanda ya shigo garin zai ga alamar masarauta a rubuce.
Ya kuma bayyana cewa akwai wasu tsare-tsare na alheri da ake shirin aiwatarwa a Masarautar Gama, yana mai fatan Allah Ya ba su damar cimma su kamar yadda aka riga aka samu nasarori a baya.

Shi ma Tafidan Gama, Alhaji Musa Yusuf Yawale, ya bayyana wa ’yan jarida cewa shekaru 25 na sarautar Dagacin Gama shekaru ne masu albarka da tarihi, inda aka samu gagarumin ci gaba a fannoni daban-daban.
Ya ce abin da suke nema yanzu shi ne Allah Ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana masu albarka.
Ya ƙara da cewa an samu ci gaba sosai a ɓangaren ilimi, musamman na Alƙur’ani, inda ya ce Gama ta yi fice wajen samar da gwanayen Alƙur’ani a faɗin Jihar Kano.
A nata ɓangaren, Jakadiyar Zaman Lafiya ta Gama, Hajiya Suwaiba Muhammad Dankabo, ta bayyana cewa an samu nasara sosai wajen zaman lafiya da juriya tsakanin al’umma masu bambancin addini, harshe da al’ada.
Ta ce duk da wannan bambanci, ana rayuwa cikin fahimtar juna da haɗin kai.
Hajiya Suwaiba ta ce ta yi aiki a Gama tsawon shekaru biyar, kuma tana alfahari da garin sakamakon jajircewar Dagacin Gama wajen inganta zaman lafiya da ɗora matasa kan tafarkin da ya dace. Ta ƙara da cewa matan Gama da Tagarji sun samu gagarumar nasara wajen sana’o’i, dogaro da kai da kuma kyakkyawar zamantakewa a cikin iyalai.

Shi ma ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, Hon. Muhammad Adamu Bomboy, ya ce babu abin da za su ce face godiya ga Allah da Ya nuna musu wannan rana ta cikar Dagacin Gama shekaru 25 kan mulki. Ya ce a wannan lokaci, Gama ta samu canje-canje masu yawa a zamantakewa da tsaro sakamakon irin salon shugabancin Dagacin.
Ya bayyana cewa a baya, Gama na fama da matsalolin daba da shaye-shaye, amma cikin ƙasa da shekaru 25, Dagacin ya kawo sauyi inda waɗannan matsaloli suka zama tarihi.
Ya ce yanzu abin da ake ji a Gama shi ne ayyukan cigaba, ƙungiyoyin ɗalibai da na tsaro.
Hon. Bomboy ya yi kira ga al’ummar Gama da su haɗa kai, tun daga ’yan siyasa, ’yan kasuwa da matasa, domin ƙara inganta tsaro, musamman ganin cewa ofishin ’yan sanda na Gwagwarwa ne ke kula da yankuna da dama ciki har da Gama.
Ya buƙaci al’umma da su yi ƙoƙarin gina wani wuri na musamman da jami’an tsaro za su riƙa amfani da shi domin ƙarfafa tsaro a yankin.

A nasa jawabin bayan karɓar shaidar karramawa, Babban Baturen ’Yan Sanda na Ofishin ’Yan Sanda na Gwagwarwa, CSP Yakubu Ƙani, ya bayyana jin daɗinsa da irin kyakkyawar dangantaka da haɗin kai da yake samu daga Dagacin Gama da masu unguwanni wajen tabbatar da tsaro.
Ya ce a wasu lokuta ma ana warware saɓani cikin gidajen masu unguwanni ba tare da kai wa ofishin ’yan sanda ba.
CSP Yakubu Ƙani ya bayyana Alhaji Rabi’u Isyaku a matsayin shugaba mai adalci da hangen nesa, yana mai yi masa fatan alheri da tsawon rai a kan sarautarsa.
Ya kuma gode da karramawar da aka yi wa rundunar ’yan sanda, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da hada kai da Masarautar Gama domin tabbatar da tsaro.
A yayin taron, an ƙaddamar da kalanda, inda mutane da dama suka bayar da gudunmawa wajen sayenta.

Haka kuma, an karrama wasu mutane bisa gudunmawar da suka bayar wajen cigaban yankin, tare da yanka kek da miƙa karramawa da iyalan Dagacin Gama suka yi masa.







