Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Sakataren Ƙungiyar Masu Fasahar Gyaran Ababen Hawa ta Ƙasa (NATA), reshen Sabuwar Kwakwacin Dawanau da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, Injiniya Alhaji Salahudeen Isma’il, ya ce garejin Sabuwar Kwakwacin Dawanau na bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓaka tattalin arziƙi da kuma samar wa dubban matasa aikin dogaro da kai a jihar Kano.
Injiniya Salahudeen ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa, inda ya ce gudunmawar da garejin ke bayarwa ba ta tsaya a Dawakin Tofa kaɗai ba, har ma ta shafi ɗaukacin fadin jihar Kano.
Ya ce ɗaya daga cikin manyan rawar da garejin ke takawa shi ne tallafa wa gwamnati wajen rage nauyin rashin aikin yi, ta hanyar ɗaukar yara da matasa marasa sana’a, musamman masu yawon talla ko zaman banza, tare da koya musu sana’o’in gyaran ababen hawa kyauta.
“A duk lokacin da muka ga yaro ko matashi da ke yawo ba tare da sana’a ba, muna tuntuɓar iyayensa domin a kawo shi garejin, inda ake koya masa sana’a, ana ba shi abinci da kuɗin mota na komawa gida, ba tare da an karɓi ko kwabo daga iyayensa ba,” in ji shi.
Ya bayyana cewa a cikin Sabuwar Kwakwacin Dawanau akwai sama da garejin gyaran mota 100, inda kowanne ke da ƙwarewa ta musamman.
A cewarsa, wasu na gyaran ƙafar gaba ko ta baya, wasu na aikin bodi, masu tada komaɗa, masu haɗa taya, gyaran fitilun mota, aikin wutar lantarki, tsarin iska da birki, da sauran fannoni masu alaƙa da gyaran ababen hawa.
Injiniya Salahudeen ya ce duk irin manyan motoci na zamani, ko daga ƙasashen Jamus, Ingila, China ko Amurka, idan aka kawo su garejin Sabuwar Kwakwacin Dawanau, da yardar Allah ana gyara su su koma aiki yadda ya kamata.
Ya ce hakan ba ya taƙaita ga manyan motoci kaɗai ba, har da ƙanana, mashina, kekuna, har ma da injinan ban-ruwa.
Ya ƙara da cewa ana ƙera dukkan nau’ikan bodin manyan motoci a garejin, ciki har da irin waɗanda ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
A cewarsa, akwai lokutan da ake kai bodin da aka ƙera a Sabuwar Kwakwacin Dawanau zuwa wasu ƙasashe, inda ake yaba wa ƙwarewar masu sana’ar.
Sai dai ya bayyana cewa babban ƙalubalen da suke fuskanta shi ne rashin tsayayyir wutar lantarki, lamarin da ke tilasta musu amfani da janareta da dizel, wanda ke ƙara tsadar aiki.
Ya ce idan gwamnati ta samar da ingantacciyar wutar lantarki, farashin ayyukan gyara zai ragu sosai, tare da ƙara bunƙasar sana’o’in da ake yi a garejin.
Ya yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa wasu ayyukan more rayuwa da ta samar, ciki har da shimfiɗa titin kwalta da ya ratsa garejin.
Ya ce ƙungiyar NATA ma tana haɗa kai wajen gyaran wasu hanyoyi domin sauƙaƙa zirga-zirga.
Injiniya Salahudeen ya ce a halin yanzu kimanin mutane 50,000 ke dogaro da ayyukan da ake yi a garejin Sabuwar Kwakwacin Dawanau kai tsaye da kuma a kaikaice.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar NATA na aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a yankin, ciki har da ƙara yawan sintirin ‘yan sanda da kuma wajabta wa kowane mai gareji ɗaukar maigadi.
Ya kuma jaddada cewa shugabancin NATA na Sabuwar Kwakwacin Dawanau na mayar da hankali wajen tabbatar da gaskiya da amana a harkar sana’a, inda duk wanda aka samu da almundahana ko rashin gaskiya ake ɗaukar matakin ladabtarwa a kansa.
A ƙarshe, ya ce a duk tarukan da suke yi, suna jan hankalin mambobinsu kan muhimmancin tsoron Allah, riƙon gaskiya da amana a sana’ar gyaran ababen hawa, domin ɗorewar sana’ar da amfanin al’umma baki ɗaya.






