Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa a harƙar man fetur, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manaja, a matsayin babban rashi ga Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
Babban Manajan Kamfanin Audu Manaja, Alhaji Sulaiman Hussain, ne ya bayyana hakan, inda ya ce ba iyalansa da na kusa da shi kaɗai ba ne za su yi kewarsa, har ma da abokan hulɗarsa a harkokin kasuwanci da sauran al’umma da suka san kyawawan halayensa.
Ya ce marigayin mutum ne mai gaskiya, riƙon amana da kuma cika alƙawari.
“Duk wanda ya san shi ba zai ce maka ya taɓa yi masa ƙarya ba. Mutum ne mai afuwa da kyakkyawar mu’amala. Mu da muke ƙarƙashinsa, ya riƙe mu kamar ’ya’yansa. Idan ka yi kuskure zai nuna maka yadda za ka gyara, kuma idan ya yi alkawari zai cika. Idan kuma wani dalili ya sa ba zai iya cikawa a kan lokaci ba, tun da wuri zai sanar da kai,” in ji Alhaji Sulaiman.
Ya bayyana cewa marigayin ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya sama da 30, maza 17 da mata 19, sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’ya’yansa mata ta rigaya ta rasu.
A cewarsa, ko da yake Alhaji Audu Manaja ya daɗe yana fama da rashin lafiya, ya yi wasu wasiyyoyi kafin tafiyarsa neman magani, lamarin da ya sa suke jin kamar ya yi hasashen cewa ba zai dawo ba.
“Mun ji zafin rashinsa matuƙa kuma muna cikin alhini. Allah Ya jikansa da rahama,” in ji shi.
Alhaji Sulaiman ya ce rasuwar Audu Manaja ta haifar da babban giɓi a harkar kasuwancin man fetur, yana mai cewa marigayin na daga cikin manyan ’yan kasuwar mai a Kano da ma Nijeriya baki ɗaya. “Rasuwarsa ta bar babban gurbi wanda zai yi wahala a cike shi cikin gaggawa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa marigayin ya mallaki gidajen mai da dama tare da ma’aikata masu yawa a sassa daban-daban na ƙasar nan.
A cewarsa, Audu Manaja yana da tankokin ɗaukar mai sama da 150, kuma kowace mota tana da direba da mataimaka.
“Idan Allah Ya kiyaye aka samu tsaiko a harkokin kamfanin, mutane da dama za su iya rasa ayyukansu.
Ban da ma’aikatan ofisoshin kamfanin da ke jihohi daban-daban na ƙasar nan,” in ji shi.
Ya ce babu shakka rasuwar Alhaji Audu Manaja ta girgiza Kano, Arewa da Nijeriya baki ɗaya, musamman a ɓangaren harkar man fetur.
Alhaji Sulaiman ya kuma gode wa ɗimbin al’ummar da suka halarci jana’izar marigayin da kuma waɗanda suka kai ziyarar ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
“Ba mu da abin da za mu ce face godiya ga duk wanda ya zo ya yi mana ta’aziyya. Muna addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayi Audu Manaja, Ya jikansa da rahama, Ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar da ya bari haƙurin jure rashinsa,” in ji shi.





