Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Hadimin Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rufa’i Sani Hanga, Hon. Nura Abubakar Maikarfi Dala, ya bayyana cewa matakin da Sanata Hanga ya ɗauka na haƙura da neman takarar Sanata domin bai wa Nasiru Yusuf Gawuna damar tsayawa takara ba sabon abu ba ne ga masu bibiyar tafiyarsa ta siyasa.

Maikarfi ya ce duk wanda ya san Sanata Hanga ya san cewa shi ɗan siyasa ne mai gwagwarmayar kawo sauyi da ci gaban al’umma, ba mutum mai neman mukami kawai ba.

“Ko lokacin zaɓen da ya gabata, Sanata Hanga ya sadaukar da takararsa aka bai wa Sanata Ibrahim Shekarau. Sai dai daga baya, cikin ikon Allah, abubuwa suka sauya har ya zama Sanatan Kano ta Tsakiya. Don haka wannan mataki da ya ɗauka yanzu ba sabon abu ba ne,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa bayan shigowar Nasiru Yusuf Gawuna cikin tafiyar Kwankwasiyya tare da magoya bayansa daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano, Sanata Hanga ya ga dacewar ba shi damar tsayawa takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

“In dai siyasa ake, bai kamata a ce an bar Gawuna ya tsaya a gefe ba. Mun yarda cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda Ya ga dama a lokacin da Ya so. Sanata Hanga ba mutum ne da ke neman mulki saboda kansa ba; yana kallon siyasa ne a matsayin hanyar yi wa jama’a hidima,” in ji shi.

Hon. Maikarfi ya ce gamsuwar da Sanata Hanga ya yi da nagarta da ƙwarewar Nasiru Yusuf Gawuna ce ta sa ya ba shi damar tsayawa takarar.

Ya ce dukkan magoya bayan Sanata Hanga sun amince da wannan mataki, domin manufar siyasa ita ce haɗa kai da kafa gwamnati mai anfani ga jama’a. “Idan aka samu nasara, babu wanda zai ji an ware shi ko an tauye masa hakkinsa,” in ji shi.

Ya jaddada cewa Sanata Hanga ya shafe sama da shekaru 50 yana harkokin siyasa, kuma a tsawon wannan lokaci yana tare da jama’a ko yana kan mulki ko ba ya kai. “Ni kaina kusan shekara 20 ke nan ina aiki tare da shi. A koyaushe yana tare da jama’a, kuma manufarsa ita ce ganin an zaɓi mutanen kirki da za su taimaka wajen rage wa al’umma wahalhalun da suke ciki,” in ji shi.

A cewarsa, manufar tafiyarsu ita ce kawo sauyi domin talaka ya amfana da dimokuraɗiyya. “Magoya bayan Sanata Hanga suna tare da shi ko da mulki ko babu. Sun yarda da irin siyasar da yake yi saboda sun gamsu da mutanen da yake mara wa baya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a tsarin Kwankwasiyya ana bai wa sauyi da gyara muhimmanci. “Idan aka ga mutanen da suke da irin wannan manufa kuma za su iya taimaka wa al’umma, ana haɗa kai da su domin a ƙarfafa tafiyar da za ta amfani jama’a,” in ji shi.

Da yake magana kan zaɓen Gwamnan Kano na 2027, Hon. Maikarfi ya ce jam’iyyar NDC ƙarƙashin tafiyar Kwankwasiyya ta tsayar da Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takararta na gwamna.

Ya ce yanzu abin da suke jira shi ne lokacin da al’umma za su yanke hukunci a akwatin zaɓe.
“Kowa ya san Gwarzo fitaccen ɗan siyasa ne wanda ya taso tun daga tushe. Mutum ne mai manufa da akida. Ya kasance Mataimakin Gwamnan Kano, amma ya ajiye mukaminsa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya saboda abin da ya yi imanin ya fi dacewa da muradun jama’a.

“Muna da yakinin cewa idan ya zama Gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2027, al’umma za su yi alfahari da jagorancinsa,” in ji shi.

A ƙarshe, Hon. Maikarfi ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe na dindindin (PVC) domin su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe a lokacin zaɓe.
Ya ce hakan ne zai ba su damar zaɓar shugabannin da suke ganin za su kawo ci gaba da sauyi ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

  • Related Posts

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Wani sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC reshen Jihar Kano, bayan wasu manyan jami’an jam’iyyar sun zargi jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso,…

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity