Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Wani sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC reshen Jihar Kano, bayan wasu manyan jami’an jam’iyyar sun zargi jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da hana ’yan takara da ba na tafiyar Kwankwasiyya ba damar samun fom domin shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Zargin ya fito ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Mohammed Rabi’u Serina, da Shugaban ADC na Jihar Kano, Hussaini Isa Mariga, suka fitar tare.
A cewarsu, an hana mambobin jam’iyyar da ba sa cikin tafiyar Kwankwasiyya damar tsayawa takara a matakai daban-daban a ƙarƙashin jam’iyyar.
Jami’an sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan Kwankwaso da magoya bayansa sun shiga jam’iyyar tare da neman ƙarin iko a tsarin shugabancinta na Kano.
Sun ce a baya shugabancin jam’iyyar na ƙasa ya shiga tsakani domin warware saɓanin, inda aka cimma matsayar cewa ɓangaren Kwankwasiyya zai riƙe kashi 60 cikin 100 na tsarin jam’iyyar, yayin da tsofaffin mambobi za su rike kashi 40 cikin 100.
“Mun amince da wannan tsari ne domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a cikin jam’iyyar. Har ma wasu daga cikinmu sun ɗauki alamomin Kwankwasiyya domin nuna kyakkyawar niyya,” in ji sanarwar.
Sai dai sun yi zargin cewa yarjejeniyar ta fara samun matsala ne lokacin rabon fom na takara.
A cewarsu, an bai wa Kwankwaso damar kula da rabon fom domin tabbatar da adalci, amma daga baya ya hana mambobin da ba na Kwankwasiyya ba damar samun fom na takarar kujerun Majalisar Jiha, Majalisar Wakilai, Sanata da kuma Gwamna.
“Mun yi ƙoƙari sau da dama domin a bai wa mambobin da ba na Kwankwasiyya ba damar samun fom, amma Sanata Kwankwaso ya ƙi amincewa,” in ji jami’an.
Sun kuma yi iƙirarin cewa har wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar ba su samu fom ba.
“Mafi muni shi ne yadda har Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano ba a ba shi damar samun fom ba,” in ji sanarwar.
Jami’an sun ce sun nemi Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Henry Seriake Dickson, da mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) su shiga tsakani, amma ƙoƙarin da suka yi na sasanta lamarin bai yi nasara ba.
“A ra’ayinmu, babu wani mutum guda da ya mallaki dukkan hikima ko cancantar jagorantar siyasa a Kano. Akwai mutane masu nagarta da za su iya lashe zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar idan aka ba su dama,” in ji sanarwar.
Haka kuma, sun musanta zargin cewa Kwankwaso ne ke ɗaukar nauyin ayyukan jam’iyyar da kudinsa.
A cewarsu, tun kafin shigowarsa jam’iyyar, ayyukan ADC a Kano suna gudana ne da gudunmawar tsofaffin mambobin jam’iyyar.
“Domin kawar da duk wani shakku, bayananmu sun nuna cewa Sanata Kwankwaso bai taɓa bayar da wata gudunmawar kuɗi ga tsarin jam’iyyar a Kano ko a matakin ƙasa ba,” in ji su.
Jami’an sun bayyana cewa ƙorafinsu ba ya nufin adawa da Kwankwaso a matsayin mutum, sai dai suna adawa da duk wani yunƙuri na mayar da kasancewa ɗan Kwankwasiyya sharaɗin shiga siyasa ko tsayawa takara a jam’iyyar.
“Mu ba mambobin Kwankwasiyya ba ne, kuma ba za mu amince a mayar da zama dan wata ƙungiyar siyasa sharaɗin shiga ko cancantar takara a jam’iyyarmu ba,” in ji su.
Sun kuma jaddada goyon bayansu ga jam’iyyar ADC tare da yin alƙawarin ci gaba da aiki tare da shugabancin ƙasa domin gina jam’iyya mai haɗa kan kowa da kowa gabanin zaɓukan da ke tafe.






