Daga Ibrahim Muhammad Kano
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta jaddada ƙudirinta na magance matsalar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar nan, idan ta samu damar karɓar ragamar mulki a zaɓukan shekarar 2027.
Mataimakin Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa mai wakiltar shiyyar Arewa maso Yamma, Malam Jafaru Sani, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai.
Ya ce jam’iyyar ADC ta tanadi ingantattun tsare-tsare da dabaru da za su taimaka wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a shiyyar Arewa maso Yamma da ma ƙasar nan baki ɗaya.
Haka kuma, ya bayyana cewa jam’iyyar na shirin yin muhimman gyare-gyare a ɓangaren shari’a domin tabbatar da adalci, zaman lafiya da doka ta yi aiki yadda ya kamata.
Malam Jafaru Sani ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su rungumi sabuwar tafiya ta jam’iyyar ADC domin ceto ƙasar nan daga halin ƙunci da take ciki, inda ya danganta matsalolin da ake fuskanta da gazawar jam’iyyar mai mulki ta APC.
A cewarsa, ADC jam’iyya ce mai hangen nesa da manufofi na gaskiya, tare da shugabanni masu jajircewa da ƙwarewa, waɗanda za su iya kawo sahihin sauyi a fannonin tsaro, tattalin arziƙi da adalci.
Jam’iyyar ADC ta yi kira ga al’ummar Arewa maso Yamma da su haɗa kai da ita domin gina ƙasa mai tsaro, adalci da cigaba mai ɗorewa.
Haka kuma, ta zargi jam’iyyar APC da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.






