Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Honarabul Sagir Abba Fagge ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da bayar da gudunmawa domin tallafa wa matasa maza da mata wajen koyon sana’o’in dogaro da kai, a daidai lokacin da ayyukan gwamnati ke ƙara yin ƙaranci.
Hon. Sagir Abba ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a taron ƙaddamar da shirin koyar da mata sana’o’i da Cibiyar Arewa ta Acquisition Skill ta shirya a ƙaramar hukumar Fagge.
Ya ce a wannan zamani, wajibi ne a karkata hankalin al’umma, musamman matasa, zuwa koyon sana’o’in hannu domin samun dogaro da kai, ganin cewa sana’a na iya samar da abin da aikin gwamnati ba zai iya bayarwa ba.
Hon. Sagir Abba ya yaba da irin ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na ɗaukar nauyin horar da mutane sana’o’in hannu, inda ya bayyana shirin a matsayin tsari mai kyau kuma ɗaya daga cikin ƙudurorin da suka ɗauki alƙawarin ƙarfafa wa al’umma.
A ƙoƙarinsa na tallafawa wannan shiri, Hon. Sagir Abba ya bayyana cewa a baya sun bayar da gudunmawar kekunan ɗinkin, kayan rini, kayan koyon yin takalma da jakunkuna. A wannan karon kuma, ya bayar da tallafin Naira dubu ɗari biyar (₦500,000) domin sayen kayan aikin da za a yi amfani da su wajen horar da mata sana’o’i.
Ya yi kira ga waɗanda za a koyar da sana’o’in da su dage su ba su muhimmanci, yana mai cewa duk abin da mutum ya koya tare da jajircewa da kyakkyawar niyya, Allah zai sanya albarka a cikinsa.
Ya ƙara da cewa matasa su tashi tsaye wajen neman sana’a, domin babu abin da ba za a samu ba idan aka yi haƙuri da jajircewa.
Dangane da kiraye-kirayen da ake yi masa na tsayawa takarar Majalisar Tarayya ta Fagge, Hon. Sagir Abba ya ce hakan na ƙara masa ƙwarin gwiwa, yana nuna al’umma na lura da ayyukan da ake yi.
Ya ƙara da cewa shi ɗan siyasa ne tun daga ƙuruciya, kuma yana ganin siyasa a matsayin hanya ta musamman wajen yi wa al’umma hidima, inda ya ce suna shirye su karɓi duk zaɓin da Allah ya yi masa.
A nasa jawabin, ɗaya daga cikin manyan malamai, Farfesa Aminu Alhassan Fagge, malami a Cibiyar Binciken Aikin Gona da Ƙananan Ruwa ta Jami’ar Bayero, Kano, ya ce lokaci ya yi da matasa ba za su riƙa dogaro da gwamnati wajen neman aiki ba.
Farfesan ya bayyana cewa hanya mafi dacewa ita ce koyar da matasa sana’o’in hannu da za su dogara da kansu, har ma su riƙa koyar da wasu.
Ya ce da irin wannan tsari, mutane da dama sun koyi ɗinki, yin takalma, jakunkuna da sauran sana’o’i.
Ya ƙara da cewa da irin tallafin da Hon. Sagir Abba ya bayar, za a horar da mata kan noma a cikin gidajensu, musamman noma na kayan lambu kamar tumatir, kokwamba da doya, ba tare da sun je gona ba.
A cewarsa, wannan zai taimaka wajen samar da sana’ar ciyar da iyali da kuma rage nauyin da ke kan maza wajen tallafawa gidajensu.






