Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ƙungiyar Arewa Acquisition Skill ta ƙaddamar da wani gagarumin shiri na koyar da mata zawarawa 1,000 sana’o’i a ƙaramar hukumar Fagge, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ta na taimakawa mata dogaro da kai a sabuwar shekarar nan.
Shugaban ƙungiyar, Sabi’u Musa Fagge, ne ya bayyana hakan yayin taron ƙaddamar da shirin horar da matan da za su amfana da wannan tsari, inda ya ce ba wannan ne karon farko da ƙungiyarsu ke ɗaukar irin wannan mataki ba na koyar da sana’o’i domin tallafa wa mata da matasa.
Ya bayyana cewa a baya sun taɓa gudanar da irin waɗannan shirye-shiryen ƙarƙashin wasu ƙungiyoyi da suka haɗa da Ƙungiyar Dogaro da Kai da kuma Sani Abacha Vocational Training, inda suke koyar da sana’o’i daban-daban ga al’umma.
Sabi’u Musa Fagge ya ce sun fuskanci ƙalubale a baya, musamman idan suka tunkari ‘yan kasuwa da sunan Sani Abacha Vocational Training, inda wasu ke ɗaukar ƙungiyar a matsayin ta gwamnati.
Wannan ne ya sa suka ga dacewar kafa sabuwar ƙungiya mai zaman kanta wadda ba ta takaita8 ga jihar Kano kaɗai ba, har ma da jihohin Arewa baki ɗaya, wadda suka sanya wa suna Arewa Acquisition Skill.
Ya ƙara da cewa ba a ƙaramar hukumar Fagge kaɗai za a aiwatar da shirin ba, domin za a riƙa zaɓen mata daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, sannan nan gaba shirin zai faɗaɗa zuwa wasu jihohin Arewa, inda a halin yanzu ake karɓar buƙatun mata masu sha’awar koyon sana’o’i.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa sana’o’in da za a koyar sun haɗa da yin takalma da jaka, ɗinki, kwalliyar mata, gyaran gashi, haɗa sabulun wankin mota, man shafawa, da sauran sana’o’i masu amfani.
Haka kuma, ya ce sun samu gudunmuwar Aminu Alhassan Fagge, malami daga Jami’ar Bayero Kano, wanda zai koyar da matan dabarun noma mai sauki da za su iya yi a gidajensu.
Ya bayyana cewa dabarar da ƙungiyar ke amfani da ita ita ce gano ƙwararru a fannoni daban-daban, tare da roƙon su su bayar da gudunmawar ilimi da ƙwarewarsu domin taimakawa mata su koyi sana’o’i.
Ya ce duk da cewa an fara shirin ne da mata, nan gaba maza ma za su amfana da irin wadannan horo.
Sabi’u Musa Fagge, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Dogaro da Kai ta Matasa da kuma Sani Abacha Vocational Association, ya gode wa masu hannu da shuni da ke ci gaba da tallafa musu, inda ya ambaci A.A. Rano a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda gudunmawarsu ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da horar da sana’o’i.
A ƙarshe, ya yi kira ga masu hali da su ƙara bayar da tallafi domin a cigaba da koyar da mata sana’o’i, yana mai cewa mace mai sana’a na iya tallafawa kanta, ‘ya’yanta da ma iyalinta gaba ɗaya, wanda hakan zai taimaka wajen rage talauci da kuma daƙile aikata abubuwan da ba su dace ba a cikin al’umma.






