Daga Ibrahim Muhammad Kano
An gudanar da wani gagarumin gangamin motsa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) tare da buɗe sabbin ofisoshin jam’iyyar a ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano, a ranar Lahadi.
Gangamin, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Gidan Mumbayya, ya samu jagorancin jigo a jam’iyyar ADC, kuma tsohon ɗan takarar Majalisar Tarayya a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Ambasada Abdulrahman Mansur Salga, wanda aka fi sani da Mainasara.
Da yake jawabi a wajen taron, Ambasada Abdulrahman Mainasara Salga, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ADC Iyali Ɗaya ta Ƙasa, ya bayyana cewa yadda jam’iyyar ADC ke samun karɓuwa a tsakanin al’umma—musamman mata da matasa—na nuni da cewa, da yardar Allah, jam’iyyar za ta samu nasara a zaɓen shekarar 2027.
Ya ce halin ƙuncin rayuwa da wahalhalun da al’ummar ƙasar nan ke ciki a ƙarƙashin jam’iyyar APC sun yi ƙamari, inda ya zargi jam’iyyar da shirin yin amfani da ƙarfin mulki da kuma kuɗaɗe masu yawa, fiye da biliyan 20, domin sayen ƙuri’un jama’a ta hanyar raba ₦50,000 ga mutum-mutum a zaɓe mai zuwa.
Ambasada Salga ya yi kira ga al’ummar ƙasar nan da su daure, kada su bari a sayi ‘yancinsu da kuɗi, yana mai jaddada cewa ba wanda zai iya yi wa mutum arziƙi face Allah.
Ya ce karɓar kuɗin da ba zai magance matsalolinsu ba, illa jefa su cikin ƙarin wahala na wasu shekaru huɗu, babban kuskure ne.
Ya ƙara da cewa, bayan dogon yawon da ya yi zuwa ƙasashe daban-daban na duniya, da ya dawo ya fahimci cewa bai dace a ce jam’iyyar ADC—wadda ke da tarin magoya baya—ba a motsa ta a ƙaramar hukumar Dala da jihar Kano ba.
Wannan ne ya sa suka fito fili domin nuna wa duniya cewa ADC na da ɗimbin magoya baya, sabanin iƙirarin cewa ba ta da ƙarfi.
Mainasara Salga ya ce tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ta lalace sakamakon kwaɗayi da son rai na wasu shugabanni, abin da ya sa suka bar ta suka koma ADC, inda suka ƙuduri aniyar yin aiki tukuru tare da jure duk wata barazana domin gina jam’iyyar.
Ya bayyana goyon bayansa ga jagoran jam’iyyar ADC, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yana mai cewa duk wanda ya fito da kyakkyawar niyya wajen gyara ƙasa, dole ne ya fuskanci jarabawa kafin samun nasara.
Ya kuma bayyana cewa shi ma yana fuskantar ƙalubale wajen tafiyar da ayyukan jam’iyyar, har da ƙoƙarin hana gudanar da wannan taro, amma duk da haka sun dage har aka gudanar da gangamin a Dala—wadda ya ce ita ce cibiyar siyasar Kano, mai cike da matasa jajirtattu.
Ambasada Salga ya ƙara da cewa bayan ziyarar da ya kai ƙasashe 18 na duniya, bai sami hutu ba bayan dawowarsa, sai ya ga ya dace a gudanar da wannan gangami domin tabbatar da tasirin ADC a jihar Kano.
Ya ce jam’iyyar na da niyyar wayar da kan jama’a su kare ƙuri’unsu, inda kowa zai zama agent na kansa domin kare akwatin zaɓensa.
Haka kuma, ya bayyana cewa ya samo wani tsari na tallafi daga ƙasashen duniya da ake bai wa ƙasashen Afirka 26, wanda za a rarraba shi ta hanyar cike fom-fom domin tallafa wa jama’a su dogara da kansu, mataki-mataki.
Ambasada Abdulrahman Mansur Salga (Mainasara) ya ce a halin yanzu ba ya neman wata takara, amma a shirye yake ya amsa kiran al’umma idan suka buƙaci ya fito takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, wadda suke fatan za ta zama mafita wajen kyautata zaman lafiya da bunƙasa cigaban ƙasa.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar ADC a matakin ƙasa, jiha da kuma ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Bayan taron, Ambasada Salga ya jagoranci tattaki daga Gidan Mumbayya zuwa wuraren da aka buɗe sabbin ofisoshin jam’iyyar ADC guda biyu—ɗaya a Unguwar Makafin Dala, ɗaya kuma a Unguwar Yalwa, Goron Dutse.






