Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jam’iyyar National NDC ta bayyana tsohon ɗan takar gwamnan Kano kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya domin zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar ta biyo bayan wata da jam’iyyar ta sanar da Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takar gwamnan Kano. Rahotanni sun nuna cewa zaɓen Gawuna ya samu ne bayan doguwar tattaunawa da shawarwari tsakanin jagororin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki a jihar.
Manufar wannan mataki, a cewar masu sharhi, shi ne ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar da kuma shirya kyakkyawar dabara wajen tunkar zaɓe mai zuwa.
Masu nazarin siyasa na kallon nadin Gawuna a matsayin muhimmin sauyi a siyasar Kano, musamman ganin kwarewarsa da gogewarsa a gwamnati. Tsohon mataimakin gwamnan ya taba rike muƙamai da dama ciki har da kwamishinan noma da kuma shugaban karamar hukumar Nassarawa.
Jam’iyyar NDC ta ce tana ci gaba da bayyana ’yan takararta na muƙamai daban-daban a matakin jiha da na ƙasa, yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ƙarfi.





