Tsofaffin Daliban Kwalejin Fasaha Ta Ungogo Sun Yaba Wa Gwamna Abba Kabir Yusuf Kan Gyaran Makarantar

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Kwalejin Fasaha ta Ungogo ta yabawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa kulawa da ɗaukin da gwamnatinsa ke bai wa Kwalejin, musamman ta fuskar gyare-gyare da farfaɗo da cibiyar.

Shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Kwalejin na ƙasa baki ɗaya, Dakta Kabir Muhammad Ibrahim, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron ƙungiyar da aka gudanar a wannan lokaci.

Ya ce taron ya kasance na farin ciki da alfahari, sakamakon irin ci gaban da Kwalejin ke samu a halin yanzu ta hannun Gwamnatin Jihar Kano.

Dakta Kabir ya ƙara da cewa a yayin taron sun karrama mutane kusan 12 bisa gudunmawa daban-daban da suka bayar wajen tallafa wa makarantar.

Ya bayyana cewa kafin a gudanar da jarabawar ƙarshe, ɗalibai na fuskantar ƙarancin kujeru, inda har babu kujera ɗaya da ɗalibi zai zauna ya rubuta jarabawa. A sakamakon haka, ƙungiyar ta nemi gudunmawa, inda aka samu kujeru guda 250.

Daga cikin waɗanda suka bayar da gudunmawar kujerun akwai Injiniya Rabiu Sufi da Injiniya Abdulƙadir Joɓe, waɗanda aka karrama a yayin taron.

Haka kuma, ya bayyana cewa ‘yan aji na shekarar 2015, duk da kasancewarsu matasa, sun samar da tutocin alwala guda 200, lamarin da ya sa aka karrama su ma.

Har ila yau, an karrama kamfanin da ke aikin gyaran makarantar, bisa la’akari da kyakkyawan aiki da kuma karɓar shawarwari da yake yi, wanda ya tabbatar da ingancin ayyukan gyaran da ake gudanarwa.

Baya ga haka, ƙungiyar ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa kulawa ta musamman da gyaran da gwamnatinsa ta yi wa makarantar, inda Dakta Kabir ya jaddada cewa tun bayan gina Kwalejin, ba ta taɓa samun irin wannan kulawa daga kowace gwamnati ba sai a wannan lokaci.

Dakta Kabir Muhammad ya bayyana cikakken goyon bayansa ga yunƙurin haɗe ƙungiyoyin tsofaffin ɗaliban makarantun fasaha na Jihar Kano wuri guda ƙarƙashin ƙungiyar KATCOSA, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunƙusa ilimin fasaha, wanda duniya ke buƙata sosai a wannan zamani.

Ya yi kira ga dukkan tsofaffin ɗalibai, ko suna da ƙungiya ko ba su da ita, da su koma makarantar da suka yi karatu su shiga ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, domin bayar da gudunmawa.

Ya ce irin wannan gudunmawa sadaka ce mai gudana, domin makarantar ita ce tushen duk abin da mutum ya zama a rayuwa.

Ya ƙara da cewa ɗaliban da ke karatu a yau ‘ya’ya da jikoki ne, kuma da a ce tsofaffin da suka gabace su ba su kula da makarantu ba, da ba za a samu damar karatu ba.

A nasa jawabin, Quantity Surveyor, Q.S. Yazid Rabiu Abubakar, wanda ke daga cikin ɗaliban farko da aka buɗe Kwalejin Fasaha ta Ungogo da su a shekarar 1984 a lokacin mulkin soja, ya ce taron ya haɗa tsofaffin ɗalibai tun daga na farko har zuwa waɗanda suka kammala karatu a baya-bayan nan.

Ya bayyana cewa taron na sada zumunci ne, domin akwai mutane da dama da tun bayan kammala karatu ba su sake haduwa ba sai a wannan taron.

Ya ce daga cikin tsofaffin ɗaliban akwai manyan ma’aikata, likitoci, injiniyoyi, ‘yan majalisar tarayya, da sauran mutane masu mukamai daban-daban a rayuwa.

Q.S. Yazid Rabiu Abubakar ya ƙara da cewa sun yi matuƙar jin daɗi ganin irin sauyin da makarantar ta samu daga yadda take a bara zuwa yanzu, inda ake gudanar da ayyukan gine-gine da gyare-gyare.

Ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa wannan yunƙuri, tare da bayyana fatan cewa tsofaffin ɗalibai za su ƙara haɗa kai wajen bayar da gudunmawa domin cigaban Kwalejin.

  • Related Posts

    An Yi Bikin Cikar Dagacin Gama Shekaru 25 Kan Mulki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano An gudanar da bikin cikar Dagacin Gama, Alhaji Rabi’u Isyaku, shekaru 25 kan karagar mulki, a fadarsa da ke garin Gama, ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar…

    Sabuwar Kwakwacin Dawanau Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Aikin Yi A Kano

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sakataren Ƙungiyar Masu Fasahar Gyaran Ababen Hawa ta Ƙasa (NATA), reshen Sabuwar Kwakwacin Dawanau da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, Injiniya Alhaji Salahudeen…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Ƙungiyar Masu Tuka Motocin Kurkura a Kano Ta Ja Hankalin Gwamnati Kan Shirin Sanya Traka Don Inganta Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Taron Ƙungiyar Masu Sayar da Abinci a Buhu: Lawan Ɓatagarawa Ya Jaddada Muhimmancin Haɗa Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Asibitin Kabir Abba Dental Care da TAT Clinic And Diagnostic Sun Duba Lafiyar Sama Da Mutane 400 A Taron Zuriyar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Muna Ganin Tasirin Taron Ƙarfafa Zumunci A Zuriyar Goronduma – Alhaji Habibu Umar Goronduma

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta

    Uwar ‘Yan-Huɗu Ta Roƙi Gwamnatin Kano Taimakon Shayar Da Jariranta