Jami’ar Bayero Na Da Kyakkyawar Dangantaka Da KASSOSA -Farfesa Haruna Musa

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An shawarci mambobin ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantun Sakandaren Kimiyya na jihohin Kano da Jigawa, wato KASSOSA, da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen halartar tarurrukan ƙungiyar a kowane matsayi da kuma duk inda suka sami kansu.

Haka kuma an buƙace su da su riƙa tunawa da makarantun da suka yi karatu a cikinsu, domin sune silar zamansu abin da suka zama a yau.

Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan yayin taron shekara-shekara na ƙungiyar KASSOSA da aka gudanar a ɗakin taron Harzabar Sabon Matsugunin Jami’ar Bayero Kano, a ranar Alhamis.

Farfesa Haruna Musa ya ƙara da cewa ya dace tsofaffin ɗalibai su riƙa yin waiwaye domin dawowa su taimaka wa makarantun da suka fito, ta yadda ƙannensu da yayansu da ke karatu a yanzu za su amfana da irin ingantaccen ilimin da su ma suka samu a baya.

Ya ce hakan zai taimaka wajen bunƙasa ilimi da kuma inganta rayuwar iyalai da al’umma baki ɗaya.

Ya bayyana farin cikinsa bisa yadda Jami’ar Bayero Kano ta zama mai masaukin baki ga taron ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantun kimiyya na Kano, KASSOSA, na ƙarshen shekara.

Ya ce abin alfahari ne ganin irin gudunmawar da mambobin ƙungiyar ke bayarwa a Jami’ar, a jihar Kano, a ƙasar nan da ma a ƙasashen waje, musamman a ɓangaren bincike da ke taimakawa al’umma tare da kawo ci gaba.

Shugaban Jami’ar ya kuma yi nuni da kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin KASSOSA da Jami’ar Bayero Kano, yana mai cewa karɓar wannan taro wata alama ce da ke nuna cewa alaƙar za ta ƙara ƙarfi, domin haɗa kai wajen taimaka wa al’umma a jihar Kano da ƙasar nan baki ɗaya.

Farfesa Haruna Musa ya bayyana cewa Jami’ar Bayero Kano ta yi fice a matakin ƙasa da na duniya, inda ƙungiyar kula da ingancin jami’o’i ta duniya ta sanya ta a matsayi na uku a Nijeriya. Sannan ta kasance ta farko a Arewacin ƙasar, kuma tana cikin manyan jami’o’i 1,200 a duniya.

Ya ƙara da cewa a ma’aunin Jami’a mai sahihancin duniya (International Outlook), Jami’ar Bayero Kano ita ce ta ɗaya a Nijeriya.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar KASSOSA na ƙasa, Balarabe Nuhu Jalla Ɗanbatta, ya ce abin da ya bambanta taron bana da na baya shi ne samun manyan baƙi daga ƙasashen waje. Daga cikin su har da Farfesa Sarki Abba, ɗalibin da ya kammala karatu tun shekarar 1984, wanda ke zaune a ƙasar Amurka, kuma ya yi fice a fagen likitanci.

Ya ce sun yi matuƙar farin ciki da halartar Farfesa Sarki Abba taron, inda ya ba ƙungiyar kulawa ta musamman, lamarin da ya ƙara ɗaga martabar taron.

Haka kuma mambobin ƙungiyar da dama sun halarta daga sassa daban-daban na ƙasar da ma ƙetare.

Balarabe Nuhu Jalla Ɗanbatta ya bayyana cewa baya ga sada zumunci da taimakon juna, ƙungiyar na da ɓangaren tallafin ilimi, inda take taimaka wa ɗalibai masu hazaka daga makarantun kimiyya na gwamnati, musamman waɗanda iyayensu ba su da ƙarfin biyan kuɗin karatu.

Ya ƙara da cewa yana alfahari da nasarorin da ƙungiyar ta samu a ƙarƙashin jagorancinsa, musamman wajen sauya tunanin shugabanci ta hanyar ɓullo da shirye-shiryen koyar da sana’o’i ga ’ya’yan mambobin ƙungiyar.

A cewarsa, sama da yara 2,000 sun koyi sana’o’i daban-daban, inda da dama daga cikinsu ke dogaro da kansu a halin yanzu.

Shi ma Shugaban Hukumar Kula da Rarraba Magunguna ta Jihar Kano (Pharmacy Council), Pharm. Ghali Sule, wanda tsohon shugaban ƙungiyar KASSOSA ne, kuma ɗaya daga cikin waɗanda aka karrama a taron, ya ce karramawar na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa gwiwar masu bayar da gudunmawa ga ƙungiyar.

Ya ce hakan na ƙara wa mutane ƙwarin gwiwar ci gaba da tallafa wa ayyukan ƙungiyar domin bunƙasarta.

Pharm. Ghali Sule ya kuma yi nuni da yadda ƙungiyar ke samun ci gaba a kai a kai, sakamakon tsare-tsare da shirye-shiryen ci gaba da shugabancin ƙungiyar ke aiwatarwa.

Ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ci gaba da ba da haɗin kai da gudunmawa domin bunƙasa ilimi a jihar Kano da ƙasar nan baki ɗaya.

  • Related Posts

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya…

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum