Asibitin Kabir Abba Dental Care tare da TAT Clinic and Diagnostic sun bayar da gudummawar duba lafiyar sama da mutane 400 a taron zuriyar Goronduma da aka gudanar a birnin Kano.
Gudunmawar ta samu ne daga Ruƙayya Kabir Abba da Wasila Aminu Goronduma, ’ya’yan zuriyar Goronduma, inda suka gudanar da ayyukan duba lafiya da kuma bayar da magunguna kyauta ga jama’a da dama, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Da take ƙarin bayani ga manema labarai, Malama Ruƙayya Kabir Abba, ma’aikaciyar lafiya, kuma shugabar Kabir Abba Dental Care, ta bayyana cewa gudunmawar da suka bayar ta ta’allaƙa ne kan faɗakarwa da kula da lafiyar baki, domin ƙara wa al’umma sani kan yadda za su kiyaye lafiyar haƙora.
Ta ce ta lura da cewa mutane da dama ba sa bai wa lafiyar baki muhimmanci, musamman batun wankin baki na asibiti da ake so a yi sau biyu a shekara (bayan kowane wata shida). Saboda haka, ta ce sun ɗauki matakin nuna wa jama’a hanyoyin da suka dace na tsaftace baki, tare da yi wa wasu wankin baki, cire haƙora, da kuma bayar da magunguna kyauta.
Ta ƙara da cewa sun zo da ƙwararrun ma’aikatan lafiya a ƙarƙashin Kabir Abba Dental Care, inda ta bayyana cewa ba a taɓa gudanar da irin wannan aikin kula da lafiyar haƙora a taron zuriyar ba sai a wannan karon, lamarin da ya haifar da gagarumin canji da amfana ga jama’a da dama.
A nata ɓangaren, Wasila Aminu Goronduma, mai TAT Clinic and Diagnostic kuma ma’aikaciya a Asibitin Kula da Masu larurar ƙwaƙwalwa na Dawanau, ta ce ta bayar da gudunmawar duba marasa lafiya kyauta ne saboda zumunci, kasancewar ’yan’uwan mahaifinta ne.
Ta bayyana cewa duk abin da ta cimma a rayuwa, iyayenta ne sila, inda ta ƙara da cewa karatun da ta yi tun tana ƙarama duk mahaifinta ne ya ɗauki nauyinsa.
Ta ce, abin takaici, Allah bai ƙaddara mahaifinta ya rayu ya ga ranar da ta fara aiki ba, domin a ranar da ta kammala karatu ne ya kwanta jinya daga bisani ya rasu.
Wannan ne ya sa ta ƙudurce a ranta cewa ba wai neman kuɗi kawai ba, har da taimakon al’umma.
Ta ce ta yi matuƙar farin ciki da taron zuriyar da aka gudanar, musamman ganin yadda aka duba lafiyar jama’a kyauta.
Ta ce duk wanda aka duba lafiyarsa zai yi addu’a da godiya, la’akari da irin wahalhalun da mutane ke fuskanta a asibitoci, ciki har da tsayuwa dogon layi ba tare da ganin likita ba, da kuma tsadar rayuwa da ke hana mutane samun ingantacciyar kulawar lafiya.
Haka zalika, Wasila Aminu Goronduma, ma’aikaciyar lafiya, ta ce sun halarci taron ne a ƙarƙashin TAT Clinic and Diagnostic, inda suka gudanar da ayyuka da dama na duba lafiya.
Ta ce sun yi gwaje-gwaje kyauta da suka haɗa da na siga (sugar), hawan jini, zazzaɓin cizon sauro, sanin rukunin jini, da sauran fannoni da dama.






