Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana cewa murabus ɗin da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya yi ya biyo bayan wasu zarge-zarge da ake yi na cewa an shirya masa maƙarkashiya domin ɓata masa suna ne.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Ambasada Yusuf Darma, ɗaya daga cikin na kusa da tsohon Mataimakin Gwamnan, inda ya ce an fara yi masa wannan shiri ne sakamakon ƙin bin Gwamnan Jihar Kano zuwa jam’iyyar APC, da kuma ƙin amincewa ya sauya aƙidarsa daga tafiyar Kwankwasiyya.
Ambasada Darma ya ƙara da cewa, ganin yadda bai bi tafiyar Gwamnan ba, hakan ya sa majalisa ta nemi buɗe bincike a kansa da nufin jingina masa wasu zarge-zarge domin ɓata masa suna, sai dai Allah ya kare shi.
Ya ce murabus ɗin da Kwamared Aminu Abdussalam ya yi ya nuna wa al’ummar Kano cewa ba shi da wani laifi, illa dai an yi yunƙurin jefa shi cikin sharri ne saboda matsayinsa na ƙin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
A cewarsa, ya zama dole ya ajiye muƙaminsa domin ganin bai dace ya ci gaba da zama a matsayin Mataimakin Gwamna ba, alhali akwai sabanin ra’ayi tsakaninsa da Gwamnan da suka zo tare aka zaɓe su.
Haka kuma ya bayyana cewa murabus ɗin nasa ya haifar da ruɗani a cikin muƙarraban gwamnati, inda har zuwa kusan mako uku ake ta ƙoƙarin nemo wanda zai maye gurbinsa.
Ambasada Darma ya jaddada cewa al’ummar Kano sun fahimci cewa zarge-zargen da aka nemi jingina wa tsohon Mataimakin Gwamnan ƙage ne, domin an san shi da gaskiya da riƙon amana.
Ya kuma yi nuni da cewa sauya sheƙar da Kwamared Aminu Abdussalam ya yi zuwa jam’iyyar ADC biyayya ce ga tafiyar Kwankwasiyya, wadda jagoranta Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.
A ƙarshe, Ambasada Yusuf Darma ya bayyana fatan cewa jam’iyyar ADC tare da jagororin Kwankwasiyya za su samu nasara a zaɓen 2027, daga matakin ƙasa har zuwa sama, da yardar Allah.





