Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa kuma tsohon Kwamishina a jihar Kano, Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa, ya bayyana cewa manufar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta sanya buƙatun al’ummar Kano a gaba, wata muhimmiyar hanya ce da za ta haifar da haɗin kai da kuma bunƙasa ci gaban jihar.

Gwagwarwa, wanda ya taɓa zama ma’ajin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kano, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai.

Ya ce jihar Kano na buƙatar samar da yanayi da zai bai wa ‘ya’yanta damar bada gudummawa, ko a cikin gida ko a ƙasashen waje, domin ci gaban jihar.

Ya jaddada cewa ya zama wajibi kowa ya sanya buƙatun Kano a gaba wajen duk wani abu da zai aikata.

“Idan aka rungumi wannan manufa ta sanya Kano a gaba, za a samu sauyi a yadda siyasa ke gudana a jihar, sabanin yadda aka saba gani a baya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a baya, bambancin siyasa da aƙida ya raba kan al’umma, inda ake fifita ra’ayoyin wasu mutane ko ƙungiyoyi fiye da muradun Kano gaba ɗaya, lamarin da ke janyo koma baya ga ci gaban jihar.

Gwagwarwa ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin sauya wannan tsari, ta hanyar ƙarfafa tunanin cewa Kano ce alƙibla ga kowa, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.

Ya yi kira ga dukkan ‘yan Kano -‘yan kasuwa, manoma, ma’aikata, likitoci da ‘yan siyasa- da su mayar da hankali wajen ba da gudummawarsu ga ci gaban jihar.

A cewarsa, manufar ba ta siyasa ba ce, illa dai kira ne ga haɗin kai, inda ya ce: “Duk inda ɗan Kano yake, ya ajiye bambancin siyasa, ya zo ya ba da tasa gudunmawar domin ci gaban Kano.”

Gwagwarwa ya kuma yi nuni da cewa tambarin jihar Kano mai ɗauke da raƙuma da dalar gyada alama ce ta ƙwazo da jajircewar Kanawa a harkokin kasuwanci da noma, wanda ya kamata a ci gaba da gina shi.

Ya gargaɗi shugabanni da kada su mayar da mulki tamkar mallakar kansu, yana mai cewa hakan na daga cikin manyan abubuwan da ke hana ci gaba.

A ƙarshe, ya bayyana cewa wannan manufa za ta taimaka wajen kawar da rarrabuwar kawuna, ƙarfafa haɗin kai, da kuma samar da kyakkyawar makoma ga matasan Kano, domin su zama shugabanni nagari a nan gaba.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum