Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da suka bayar da gagarumar gudunmuwa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Najeriya.
Taron karramawar, wanda aka gudanar a Babban Ɗakin Karatu na Murtala Muhammad da ke jihar Kano, ya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban na ciki da wajen jihar.
Daga cikin mahalarta taron akwai manyan masu sarautun gargajiya, jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya, ƙungiyoyi da sauran al’umma daga kabilu daban-daban.
Daya daga cikin waɗanda aka karrama ita ce Ambasada Dakta Nana Maryam Abubakar Gwambe, wadda aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin fitattun mata masu bayar da gudunmuwa wajen tallafa wa al’umma da inganta zaman lafiya.
Da take zantawa da manema labarai bayan karramawar, Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe ta bayyana matuƙar farin cikinta, inda ta ce karramawar ta zo mata ne a bazata.
“Babu abin da zan ce sai dai in gode wa Allah da ya nuna min wannan rana. Haƙiƙa na ji farin ciki matuƙa, domin abu ne da ban taɓa tsammani ba. Wannan karramawa ta sa na ƙara alfahari da irin tarbiyyar da iyayena suka ba ni,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa duk wani kyakkyawan hali da take nunawa da kuma ayyukan alheri da take yi, ta samo su ne daga tarbiyyar da iyayenta suka gina mata tun tana karama.
Har ila yau, ta bayyana cewa wannan karramawa ta ƙara mata ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da taimakawa al’umma da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.
Ambasada Dakta Nana Maryam Gwambe ta kuma shawarci ƙungiyar WAZOBIA da ta ci gaba da zaƙulo mutane masu hazaƙa da kuma karrama su, domin hakan na kara ƙarfafa musu gwiwa.
Ta ce irin wannan ƙoƙari na taimakawa wajen karfafa haɗin kan al’umma da kuma inganta zaman lafiya ba tare da la’akari da bambancin ƙabila, addini ko harshe ba, kamar yadda taken Nijeriya ke nuni da haɗin kai.







