Naɗin Sarautar Ajiyan Kano Karramawa Ce Gareni -Alhaji Muhammad Sunusi Bello

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sabon Ajiyan Kano, Alhaji Muhammad Sunusi Bello, wanda Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya naɗa a fadarsa ranar Juma’a, ya bayyana cewa naɗin da aka yi masa wata babbar karramawa ce da aka yi masa bisa yarda da amincewa da shi.

Da yake zantawa da manema labarai bayan naɗin, ya ce farin cikinsa ba zai misaltu ba, musamman idan aka yi la’akari da irin kalaman yabo da hujjojin da Sarkin ya bayyana game da shi yayin bikin naɗin.

Ya ce duk wanda ya halarci bikin naɗin zai fahimci irin karramawar da aka yi masa, domin kalaman da Sarkin ya yi sun nuna gamsuwa da cancantarsa, abin da ya ƙara masa farin ciki fiye da sarautar kanta.

Sabon Ajiyan Kanon ya ƙara da cewa, a cikin hakiman Kano da yawansu ya kai kusan 74, Sarkin ya zaɓe shi ya ba shi wannan sarauta, wanda ya bayyana a matsayin babbar nasara da ba zai iya bayyana ta da baki ba.

Ya ce abin da ya rage musu shi ne ci gaba da yi wa Sarkin addu’a, yana roƙon Allah Ya tsare mutuncinsa, Ya ƙara masa lafiya, nasara da kuma tsawon rai.

Har ila yau, ya bayyana cewa sarautar “Ajiya” ba a ba ta sai ga wanda aka amince da shi, yana mai cewa duk wanda Sarkin Kano ya ba wannan mukami, to yana nuni da cewa an yarda da gaskiyarsa, amincinsa da kuma rikon amanarsa.

Dangane da tarihin sarautar, Alhaji Muhammad Sunusi Bello ya ce a da ba a da wannan sarauta a Kano, sai a zamanin marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero ne aka fara ƙirƙiro ta, inda aka fara naɗa Alhaji Muhammadu Ɗansarari, bayan rasuwarsa sai ɗansa Aminu Ɗansarari ya gaje shi. Daga bisani kuma aka naɗa Ja’afar Shanono, kafin yanzu da aka naɗa shi a matsayin Ajiyan Kano na huɗu a tarihin sarautar.

  • Related Posts

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta…

    Gwamnan Zamfara Ya Buƙaci A Ƙara Addu’o’in Zaman Lafiya Yayin Bikin Babbar Sallah

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga al’ummar jihar da ma ɗaukacin Nijeriya da su ƙara dagewa wajen yin addu’o’in zaman lafiya da tsaro a yayin bikin Babbar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya