Sanatan Kano Ta Tsakiya: An Ƙaddamar Da Garba Yusuf Abubakar A Jam’iyyar APC

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana Malam Garba Yusuf Abubakar a matsayin mutum mai ilimin addini da na zamani, mai amana, kuma ƙwararre a fannin siyasa da aikin gwamnati.

An ce ya taɓa zama Kwamishina har sau biyar ba tare da an taɓa samun sa da almundahana ba.

Wannan ne ya sa jama’a suka ba da shawara tare da yin kira gare shi da ya fito ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

Hon. Muntari Ishak Yakasai, Darakta Janar na yakin neman zaɓen Malam Garba Yusuf Abubakar na neman takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ne ya bayyana hakan a taron kaddamar da takararsa da aka gudanar a yammacin ranar Lahadi a harabar ofishin Tinubu Support Groups na Kano.

Ya ce idan Malam Garba Yusuf ya zama Sanatan Kano ta Tsakiya, al’umma ba za su yi da-na-sani ba, domin zai bai wa Gwamnan Kano haɗin kai domin su yi aiki tare wajen kawo ayyukan alheri a mazabar Kano ta Tsakiya.

Hon. Muntari Ishak ya ce sun karɓi Garba Yusuf Abubakar a matsayin ɗan takara kuma za su ba shi cikakken goyon baya domin ya zama ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya. Ya ƙara da cewa, in Allah Ya yarda, za su tabbatar da nasararsa, sannan ya buƙaci magoya baya su tashi tsaye domin yin aiki don samun nasara.

A nasa jawabin, Malam Garba Yusuf Abubakar, wanda ya fito neman takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, ya gode wa Allah da Ya ba shi wata baiwa da bai taɓa tunanin zai samu ba.

Ya ce an yi shawara aka ce ya fito ya tsaya takarar Sanata, kuma da ya kalli girman nauyin wannan aiki, sai waɗanda suka ba shi shawarar suka ce za su taimaka masa ko da a kafaɗa ne har sai an kai ga nasara. Saboda haka ya amince suka shiga wannan gwagwarmaya hannu bibbiyu.

Malam Garba Yusuf Abubakar ya jaddada godiyarsa ga waɗanda suka ƙaddamar da wannan takara, sannan ya roƙi magoya bayansa da duk wanda zai yi amfani da sunansa da kada ya yi abin da bai dace ba.

Ya ce bai yarda da siyasar zage-zage ba, yana son a gudanar da komai cikin mutunci.

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugaban Tinubu Support Group, Hon. Baffa Babba Ɗan Agundi, shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, Hon. Salim Hashim, da sauran ’yan siyasa da dama.

  • Related Posts

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta…

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a jam’iyyar APC kuma ɗaya daga cikin hadiman tafiyar siyasar Hon. Hassan Shehu Hussain, ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya