Ƙungiyar KAPAG Ta Ziyarci Shugaban Ƙaramar Hukumar Tarauni, Kano, Ta Jaddada Goyon Baya Ga APC

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar KAPAG da ke ƙarƙashin jagorancin Hajiya Balaraba Ibrahim ta kai ziyara ga shugaban ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano, Hon. Sekure, a sakatariyar ƙaramar hukumar, ranar Litinin.

Hajiya Balaraba Ibrahim ta bayyana cewa ziyarar na daga cikin jerin matakan da ƙungiyar ke ɗauka na jaddada goyon baya ga jam’iyyar APC, musamman biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin dawowar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, jam’iyyar APC.

Ta ce ƙungiyar KAPAG, ƙungiya ce ta siyasa daga tushe, wadda ta shafe sama da shekaru 25 tana aiki tare da jama’a, tana bibiyar al’amuran siyasa tun daga matakin ƙasa.

A cewarta, hakan ne ya sa suka ga dacewar bin tafarkin jam’iyyar APC tare da dukkan waɗanda suka haɗu a cikinta domin cigaban Kano.

Hajiya Balaraba Ibrahim ta ƙara da cewa sun fara wannan shiri ne da ziyarar shugaban ƙaramar hukumar Tarauni domin jaddada goyon baya gare shi, kamar yadda suka saba tun a baya.

Ta ce yanzu da aka sake haɗuwa a jam’iyya guda, babu dalilin rarrabuwar kai, illa haɗa ƙarfi da ƙarfe domin amfanin al’ummar Tarauni da jihar Kano baki ɗaya.

Shugabar ta yi kira ga ‘yan jam’iyya a matakin ƙasa da shugabanni, musamman a Tarauni, da su guji rikice-rikicen siyasa marasa amfani.

Ta jaddada cewa neman muƙami abu ne na kowa, kuma Allah Shi ne Mai bayarwa, don haka bai dace ‘yan jam’iyya su zama maƙiya juna ba.

Ta ce ƙungiyar KAPAG za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar APC cikakken goyon baya ɗari bisa ɗari, tana mai cewa bambancin ra’ayi a siyasa abu ne na ɗabi’a, kamar yadda yake faruwa ko a cikin gida ɗaya, amma hakan bai kamata ya hana mutunta juna ba.

Hajiya Balaraba Ibrahim ta bayyana cewa sukan ajiye siyasa a gefe idan ana mu’amala ta zamantakewa, inda suke halartar bukukuwa da jaje ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.

Ta ce duk abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, suna kallon sa a matsayin na ɗan gida da ya dawo gida.

Ta ƙara da cewa wannan ita ce ziyararsu ta farko zuwa ƙaramar hukumar Tarauni, haka kuma ziyarar da suka kai gidan gwamnatin Kano kwanakin baya ita ce ta farko tun bayan kammala wa’adin tsohuwar gwamnatin Kano ƙarƙashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, har zuwa lokacin da aka karɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC.

Hajiya Balaraba Ibrahim ta yaba wa Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa jajircewarsa da rawar da ya taka a matsayin uba da jagora, wajen tabbatar da dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC.

Ta yi masa fatan kammala aikinsa lafiya, tare da roƙon Allah Ya bai wa Kano zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A ƙarshe, ta ce ƙungiyar KAPAG za ta ci gaba da kai ziyara lungu da saƙo a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano domin jaddada goyon baya ga jam’iyyar APC da shugabanninta, har zuwa zaben 2027, inda ta bayyana fatan jam’iyyar za ta samu nasara da ikon Allah.

  • Related Posts

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Asibitin Ƙashi na Tarayya da ke Dala, Kano, ya ba wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi, Hon. Abba Kabir Bichi, lambar karramawa bisa gudunmawa…

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gidauniyar NNPCL, reshen ayyukan jin ƙai na NNPC Ltd, ta ƙaddamar da sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani mai ƙarfin 1.5 Tesla MRI Scan da aka…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity