Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Asibitin Ƙashi na Tarayya da ke Dala, Kano, ya ba wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi, Hon. Abba Kabir Bichi, lambar karramawa bisa gudunmawa da goyon bayan da yake bayarwa wajen bunƙasa ayyukan asibitin.
An gabatar da lambar karramawar ne a yayin bikin ƙaddamar da sabuwar na’urar binciken cututtuka ta zamani (MRI Scan) da Gidauniyar NNPCL ta samar wa asibitin a ranar Alhamis.
Dakta Muktar Nura Bichi, shugaban kwamitin ilimi na ofishin ɗan majalisar kuma mai kula da shirin tura ɗalibai karatu ƙasashen waje, ne ya wakilci Hon. Abba Kabir Bichi wajen karɓar lambar karramawar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan karɓar lambar, Dakta Muktar ya ce gudunmawar da Hon. Abba Kabir Bichi ke bayarwa ba ta taƙaitu ga Asibitin Ƙashi na Dala kaɗai ba, domin yana tallafa wa ayyukan bunƙasa harkar lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya ce, “A duk inda ake gudanar da ayyukan da suka shafi harkar lafiya a faɗin Nijeriya, Hon. Abba Kabir Bichi yana bayar da gudunmawarsa. Kasancewarsa Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, ya taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ayyukan da ake aiwatarwa a asibitocin gwamnati da dama.”
Ya ƙara da cewa wannan karramawa wata alama ce da ke nuna cewa al’umma da masu amfana da ayyukansa suna yaba wa irin gudummawar da yake bayarwa.
“An ce yaba wa mutum tukuici ne gare shi. Hon. Abba Kabir Bichi ya samu lambobin karramawa da dama daga cibiyoyi da ƙungiyoyi daban-daban saboda ayyukan alheri da yake yi,” in ji shi.
Dakta Muktar ya bayyana cewa babban burin Hon. Abba Kabir Bichi shi ne inganta rayuwar al’ummarsa, da ci gaban Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya ta hanyar tallafa wa ayyukan raya ƙasa.
Ya ce Asibitin Kashi na Dala na da matsayi na musamman a wurin ɗan majalisar, yana mai tabbatar da cewa akwai ƙarin manyan ayyukan ci gaba da ake sa ran za a samar wa asibitin domin ƙara inganta ayyukan kula da marasa lafiya.
Haka kuma ya bayyana cewa Hon. Abba Kabir Bichi ya taimaka wajen saka muhimman ayyukan raya ƙasa da dama a cikin kasafin kuɗin tarayya, waɗanda za su amfani Jihar Kano da Nijeriya gaba ɗaya.






