Abdurrahman Mainasara Salga Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin ADC A Dala Da Kuri’u 8,973

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An gudanar da zaɓen fid-da-gwani na neman tsayawa takarar kujerar majalisar tarayya ta ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ranar 21 ga Mayu, 2026.

Zaɓen ya gudana ne bisa tsarin “ƙato bayan ƙato” kamar yadda dokar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tanada, inda aka bayyana cewa an gudanar da shi cikin lumana da kwanciyar hankali.

’Yan takara uku ne suka fafata a zaɓen, waɗanda suka haɗa da Hon. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga, Hon. Nasir Isa da Hon. Bashir Muhammad.

An gudanar da zaɓen ne ƙarƙashin kulawar wakilan uwar jam’iyyar ADC ta ƙasa, ƙungiyoyin sa ido da jami’an tsaro, yayin da mambobin jam’iyyar maza da mata suka fito domin kaɗa ƙuri’unsu.

Bayan kammala zaɓen, kwamitin gudanarwa ya bayyana sakamakon kamar haka: Hon. Nasir Isa ya samu ƙuri’u 821, Hon. Bashir Muhammad ya samu ƙuri’u 1,584, yayin da Hon. Amb. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga ya samu ƙuri’u 8,973.

Jimillar ƙuri’un da aka kaɗa sun kai 11,377.

Bisa ga wannan sakamako, an bayyana Hon. Amb. Abdurrahman Mansur Mainasara Salga a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC domin tsayawa takarar kujerar majalisar tarayya ta Dala a zaɓen shekarar 2027.

Da yake magana bayan ayyana sakamakon zaɓen, Hon. Abdurrahman Mainasara Salga ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da ya samu, inda ya danganta hakan da goyon bayan da mambobin jam’iyyar ADC a Dala suka ba shi.

Ya kuma yi kira ga sauran ’yan takarar da suka fafata da shi da su haɗa kai domin mara wa jam’iyyar ADC baya, domin tabbatar da nasararta a zaɓen 2027.

  • Related Posts

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta…

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a jam’iyyar APC kuma ɗaya daga cikin hadiman tafiyar siyasar Hon. Hassan Shehu Hussain, ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya