Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Hon. Abdurrahman Mansur Salga Mainasara ya miƙa godiyarsa ga Allah da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Dala, Kano, musamman mambobin jam’iyyar ADC, bisa fitowar da suka yi a zaɓen fidda gwani domin nuna masa goyon baya da ƙauna.
Salga ya bayyana cewa tun farko bai taɓa sha’awar shiga siyasa ba, amma a matsayinsa na ɗan kasuwa, yakan yi tunanin halin rayuwar al’umma da ƙalubalen da suke fuskanta.
Ya ce hakan ne ya sa ya ga dacewar tashi domin ba da gudunmawa wajen taimaka wa mutanen Dala su samu hakkokinsu.
“Na zagaya lungu da saƙo na Dala tun ina ƙarami, daga Madabo, Adakawa, Limanchi, Kofar Mazugal, Ƙoƙi da sauran sassa. Lokacin da na ga damar da Allah Ya ba ni, sai na tambayi kaina me zai hana in mayar da wannan dama domin amfanar al’umma,” in ji shi.
Hon. Salga ya ce a ranar zaɓen fidda gwani na ADC, maza da mata sun fito duk da ruwan sama domin kaɗa masa ƙuri’a ba tare da ya ba su kuɗi ba, har ma da na mota ko na shan ruwa.
Ya ce al’ummar sun bayyana masa cewa suna yin hakan ne saboda gaskiya da kuma ƙudirinsa na ganin an samu ci gaban Dala.
Ya ƙara da cewa ya yi addu’a ga Allah yana cewa: “Ya Allah, idan Ka ba ni wannan mulki, kada Ka bar ni da ƙarfina kaɗai. Ka taimake ni in taimaki al’umma. Ba na son mulki, amma ina ganin ƙaddara ta ce za ta kai ni ga haka.”
Salga ya kuma tunatar da cewa tun farko bai nemi sauran ’yan takara su janye masa ba, domin a cewarsa har ya yi tunanin barin musu damar.
Sai dai ya ce ya ji tausayin al’umma bayan ganin yadda suka fito cikin ruwan sama suka kaɗa masa ƙuri’a cikin lumana ba tare da wata hatsaniya ba.
“Don haka ina roƙon Allah, idan Ya ba ni wannan dama, in yi adalci. Kuma ina addu’ar duk wanda ya samu wata dama, Allah Ya taimake shi ya kawo ci gaba ga al’umma,” in ji shi.






