Al’ummar Kano Ta Tsakiya Sun Bukaci Balarabe Sorondinki Ya Tsaya Takarar Sanata A ADC

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Al’ummar ƙananan hukumomi 15 da ke mazaɓar Kano ta Tsakiya sun yi kira ga Shugaban Matasan Jam’iyyar ADC na ƙasa, Hon. Balarabe Rufa’i Soronɗinki, da ya fito takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen shekarar 2027.

Masu kiran sun bayyana Balarabe Rufa’i Soronɗinki a matsayin matashi mai nagarta, kishin al’umma da kuma jajircewa wajen kawo ci gaba daga tushe.

Sun ce sun gamsu da irin ƙwazonsa da sadaukarwarsa wajen tabbatar da an samu sauyi mai amfani ga al’umma, tare da bayyana cewa tsayawarsa takara zai taimaka wajen samar da ci gaba mai dorewa a mazabar Kano ta Tsakiya.

Haka kuma, sun yabawa rawar da yake takawa a jam’iyyar ADC, musamman wajen bai wa matasa dama a harkokin siyasa da kuma ƙoƙarinsa na bunƙasa jam’iyyar ba tare da gajiyawa ba.

A cewarsu, irin gudunmawar da yake bayarwa ga jam’iyyar da al’umma ya nuna cewa ya cancanci wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

Masu ruwa da tsaki na ADC a Kano ta Tsakiya sun kara da cewa lokaci ya yi da Balarabe Soronɗinki zai amsa kiran al’umma domin tsayawa takarar kujerar Sanata.

“Jam’iyyar ADC ta bayyana aniyarta ta bai wa matasa damar tsayawa takarar kujerar Sanata a kowace jiha, kuma a Kano ta Tsakiya, Balarabe Rufa’i Soronɗinki ne zaɓin al’umma. Muna kira gare shi da ya amsa wannan kira,” in ji su.

  • Related Posts

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta…

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a jam’iyyar APC kuma ɗaya daga cikin hadiman tafiyar siyasar Hon. Hassan Shehu Hussain, ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya