PDP Kano Na Shirin Fitar Da ‘Yan Takara A Matakai Daban-Daban — Hon. Rabiu Saleh Wangal

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana shirin fitar da ‘yan takara a matakai daban-daban na kasa da jihohi, yayin da ta fara sayar da fom ɗin takara daga kujerar shugaban ƙasa zuwa sanatoci, gwamnoni, ‘yan majalisar tarayya da kuma na jihohi.

Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kano, Hon. Rabiu Saleh Wangal, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.

Ya ce a halin yanzu jam’iyyar ta kafa sakatariya da kuma kwamitoci a matakin jihar domin kula da tsarin sayar da fom, inda ‘yan jam’iyya ke ci gaba da zuwa domin sayen fom na takara a matakai daban-daban.

Hon. Wangal ya bayyana cewa a wannan karon PDP ta ɓullo da sabon tsari domin hana ‘yan takara zuwa da dumbin magoya baya wajen sayen fom.

“Zuwo da mutane masu yawa domin sayen fom ba ya cikin tsarinmu. Muna gudanar da harkokinmu cikin mutunci da tsari,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa a wuraren da ake samun masu neman takara da yawa a kujera ɗaya, jam’iyyar ta kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban PDP na Jihar Kano, Alhaji Ali Karza, domin sasanta bangarorin tare da zakulo dan takara guda daya mafi cancanta.

A cewarsa, tuni an samu sulhu tsakanin masu neman takara a ƙananan hukumomi da dama, kuma dukkansu sun karbi fom dinsu na takara.

Hon. Rabi’u Saleh Wangal ya jaddada cewa PDP a jihar Kano jam’iyya ɗaya ce ƙarƙashin shugabancin Injiniya Dakta Bello Gambo Bichi, yana mai cewa duk wanda ke son tabbatar da sahihin shugabancin jam’iyyar zai iya duba portal na INEC.

“Duk wanda ya kira kansa shugaban jam’iyya ba tare da INEC ta tabbatar da shi ba, idan aka kai shi kotu za a hukunta shi,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa uwar jam’iyyar PDP ta ƙasa bisa haɗin kai da ake samu a Kano, inda ya ce ana ci gaba da samun kwararowar sabbin mambobi zuwa jam’iyyar daga wasu jam’iyyun siyasa saboda rashin damar dimokiradiyya a cikinsu.
“A PDP ne ake bin tsarin dimokiradiyya da bai wa kowa dama,” in ji shi.

Hon. Wangal ya bayyana cewa jam’iyyar ta samar da rangwame ga mata da matasa masu sha’awar tsayawa takara.

A cewarsa, mata za su biya kaso biyar cikin ɗari na kuɗin fom, yayin da matasa masu ƙasa da shekara 40 za su biya kaso 50 cikin ɗari na kuɗin fom da jam’iyyar ta ƙayyade.

Dangane da ficewar wasu jiga-jigan PDP daga jihar Kano, Wangal ya ce hakan ba zai kawo wa jam’iyyar cikas ba.
“Ba jiga-jigai ne kaɗai ke tafiyar da jam’iyya ba. Matasa maza da mata ne ke fita suna tallata PDP. Har yanzu suna tare da mu, kuma da yardar Allah PDP za ta lashe zaben jihar Kano tare da kafa gwamnati,” ya bayyana.

A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Kano da su zabi shugabanni nagari masu cancanta maimakon bin siyasar biyayya ga wasu mutane.
“Muna kira ga duk wanda zai iya bayar da gudunmawa ya zo mu haɗa kai domin tallafa wa ‘yan takarar PDP su samu nasara,” in ji shi.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum