Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Borno mai wakiltar ƙaramar hukumar Bayo a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Hon. Usman Muhammad Garba, ya bayyana cewa amsa kiran al’umma ne ya sa ya fito takara domin wakiltar mutanen yankinsa.
Hon. Usman ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce ya ɗauki matakin fitowa takara ne bayan ganin yadda al’umma ke ci gaba da fama da matsaloli sakamakon shugabancin da ba ya amfani da muradun jama’a.
Ya ce tun daga shekarar 1999 yake fafutukar siyasa a matsayinsa na matashi mai kishin al’umma, kuma yanzu lokaci ya yi da zai tsaya domin kare martaba da dimokraɗiyya a ƙaramar hukumar Bayo da jihar Borno baki ɗaya.
“Akwai mutane da al’umma ke ɗorawa a gaba, amma daga ƙarshe sukan sayar da ‘yancin jama’a domin biyan buƙatun kansu. Wannan ne ya sa muka ga lokaci ya yi da za mu fito mu tsaya takara domin kawo sauyi,” in ji shi.
Ya bayyana cewa duk da daɗewar da ake yi ana mulkin dimokraɗiyya a Nijeriya, har yanzu matasan Borno ba su amfana da ita yadda ya kamata ba.
“A mafi yawan jihohin Nijeriya ana shan romon dimokraɗiyya, amma a Borno har yanzu mutane da dama ba su san ma’anar wakilci nagari ba. Wasu matasa ma idan ranar dimokraɗiyya ta zo, maimakon farin ciki sai su yi tunanin halin da suke ciki,” ya ce.
Hon. Usman ya ce rashin shugabanci nagari da kuma kakaɓa shugabanni ba tare da la’akari da cancanta ba na daga cikin abubuwan da suka jefa jihar cikin matsaloli.
Ya ƙara da cewa mafi yawan shugabannin da suka wakilci yankin a baya sun fi mayar da hankali kan abin da za su amfana da shi tare da iyalansu, maimakon ci gaban al’umma.
A cewarsa, ƙaramar hukumar Bayo na daga cikin yankunan da suka fi fama da ƙarancin ci gaba a jihar Borno, inda ya ce rashin ingantaccen wakilci ya hana yankin samun muhimman ayyukan raya ƙasa da mukamai masu amfani.
“Mutane da dama da aka bai wa damar wakiltar al’umma ba su san ma’anar kujerar da suke kai ba. Abin da kawai suka sani shi ne abin da za su samu,” in ji shi.
Ya ce idan aka ba shi dama, zai yi amfani da kujerar wajen dawo da martabar ƙaramar hukumar Bayo tare da wayar da kan matasa game da muhimmancin siyasa da wakilci na gari.
Hon. Usman ya yi alƙawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa matasa wajen samun ilimi, aikin yi, sana’o’in dogaro da kai da kuma guraben aiki.
Ya kuma ce jam’iyyar ADC na da manufofin kawo sauyi a jihar Borno, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa al’umma za su mara musu baya a zaɓen 2027.
Dangane da matsalolin tsaro, rashin aikin yi da rashin ilimi da ake fama da su, ɗan takarar ya ce al’umma na da rawar da za su taka wajen kawo canji ta hanyar zaɓen shugabanni nagari.
Ya gargaɗi masu jefa ƙuri’a da su guji sayar da ƙuri’unsu saboda kuɗi ko kayan masarufi.
“Wasu sukan zo ranar zaɓe su ba mutane kuɗi ko kayan abinci domin su sayi ƙuri’unsu. Wannan shi ne babban abin da ya jefa al’umma cikin matsaloli. Kuɗin da ake bayarwa kuɗin jama’a ne,” in ji shi.
Sai dai ya shawarci al’umma da su karɓi duk abin da aka ba su idan hakan ta taso, amma su zaɓi ɗan takarar da suka yarda zai kawo ci gaba.
A ƙarshe, Hon. Usman Muhammad Garba ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Bayo da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe tare da fitowa ranar zaɓe domin kare ƙuri’unsu da kuma zaɓar jam’iyyar ADC a matsayin hanyar kawo sauyi a yankin.






