Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Dan takarar majalisar jiha na Tarauni karkashin jam’iyyar NDC Kwankwasiyya, Hon. Sagir Wada Sinkin Mai Iyali, ya yabawa al’ummar Kano kan ci gaba da tsayawa kyam da suke kan goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya da ‘yan takararta.
Hon.Sinkin ya bayyana hakan ne bayan ganawar da magoya baya da ‘ya’yan jam’iyyar NDC suka yi a gidan jagoran Kwankwasiyya. A wani taro da aka tattauna yadda za a kara karfafa hadin kai da cigaban tafiyar.
Ya mika godiya ta musamman ga daukacin al’ummar Kano bisa yadda suke ci gaba da yarda da kuma fitowa domin tallafawa tafiyar NDC Kwankwasiyya
Ya kara da cewa irin karbuwar da tafiyar ke samu a Kano sakamako ne na manufofin tafiyar kwankwasiyya na kishin kasa da kokarin inganta rayuwar talakawa. Wannan tasa jama’a ke gamsuwa da nuna amincewa da tafiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi na neman shugabancin kasarnan.
Hon.Sagir Wada Sinkin ya yi kira ga magoya baya na karamar hukumar Tarauni da jihar Kano gaba daya akan su ci gaba da hada kai da baiwa tsarin tafiyar kwankwasiyya da jam’iyyar NDC goyon baya domin tabbatar da cimma burin da aka sanya gaba.
Ya yi nuni da cewa karuwarda ake sanu na tafiyar Kwankwasiyya a Kano dama kasa baki daya wata alama ce ta cewa jama’a sun gamsu da shirin jam’iyyar NDC na kawo sauyi mai muhimmanci da ma’ana.
Taron da aka gudanar ya samu halartar ‘yan jam’iyya daga karamar hukumar Tarauni da makwabtan ta, inda dukkan su suka tabbatar da ci gaba da aiki tare domin samun nasara a zabe mai zuwa.






