Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Al’ummar ƙananan hukumomin Ungogo da Minjibir a jihar kano sun bayyana gamsuwarsu da wakilcin da Hon. Sani Adamu Wakili ke yi musu a Majalisar Tarayya, tare da kira ga jam’iyyar NDC da ta sake tsayar da shi takara a zaɓen 2027.
Wani mazaunin unguwar ‘Yar’adua da ke ƙaramar hukumar Ungogo, Alhaji Ibrahim Usman Ali Meshelia, ne ya bayyana hakan yayin da yake yabawa irin ayyukan ci gaban da ɗan majalisar ke aiwatarwa a yankunan biyu.
Ya ce tun bayan kafuwar mazaɓar Ungogo da Minjibir, ba a taɓa samun wakilin da ya kawo sauye-sauye da tallafi ga al’umma kamar Hon. Sani Adamu Wakili ba.
A cewarsa, ɗan majalisar ya taimaka wa matasa da dama ta hanyar rabon motoci, babura da Adaidaita Sahu kyauta domin rage rashin aikin yi da bunƙasa sana’o’i.
Haka kuma, ya ce Hon. Sani Adamu Wakili ya bai wa mata tallafin jari domin fara ƙananan sana’o’i, abin da ya bayyana a matsayin wani babban ci gaba ga rayuwar iyalai a yankin.
Meshelia ya ƙara da cewa ɗan majalisar na bayar da muhimmanci sosai ga harkar ilimi, inda yake ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a makarantun kimiyya da sauran manyan makarantu.
Ya kuma bayyana cewa a lokutan Azumi da bukukuwan Sallah, Hon. Sani Adamu Wakili kan raba kayan abinci da tallafin kuɗi ga al’umma a faɗin Ungogo da Minjibir.
“Mutanen Ungogo da Minjibir suna goyon bayan Hon. Sani Adamu Wakili kashi 100 bisa 100, kuma muna ci gaba da bin tafarkin jagorancin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a ƙarƙashin jam’iyyar NDC,” in ji shi.
Ya ce ɗan majalisar mutum ne mai sauraron koke-koken jama’a, inda ya bayyana cewa kofarsa a buɗe take domin karɓar baƙi da sauraron matsalolin al’umma a kowane lokaci.
Kazalika, ya ce Hon. Sani Adamu Wakili na gabatar da kudurori da ayyukan ci gaba da suka haɗa da gina hanyoyi da samar da fitilun hasken rana a yankuna da dama na Ungogo da Minjibir.
“Yanzu idan ka shiga wasu sassan yankin da dare, za ka ga tamkar da rana ne saboda hasken fitilun da aka girka,” in ji Meshelia.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Ungogo da Minjibir da su ci gaba da mara wa Hon. Sani Adamu Wakili baya tare da sake zaɓensa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC a shekarar 2027 domin ci gaba da ayyukan raya yankin.








