Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jagoran Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wani zama na sulhu da ya haɗa manyan jiga-jigan jam’iyyar biyu daga Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibrin da tsohon Ministan Gidaje, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo.
Zaman, wanda ya gudana a gidan gwamnatin Kano, ya kasance na ƙarshe cikin jerin tattaunawar da aka shafe lokaci ana yi domin tabbatar da haɗin kai da ƙarfafa jam’iyyar APC a jihar.
A yayin zaman, tsohon Ministan Gidajen, ATM Gwarzo, ya bayyana janyewa daga aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata domin bai wa Sanata Barau Jibrin cikakken goyon baya a zaben da ke tafe.

Rahotanni sun nuna cewa matakin ya samu karɓuwa daga shugabanni da magoya bayan jam’iyyar, inda suka bayyana hakan a matsayin wani babban ci gaba wajen haɗa kan APC musamman a yankin Kano ta Arewa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu ta ce, zaman ya nuna yadda shugabannin jam’iyyar APC ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna da kuma ɗorewar haɗin kai tsakanin manyan ‘ya’yanta.







