Gwamnatin Kano Ba Ta Da Niyyar Cire Sarki Muhammad Sanusi

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ƙaryata Rahoto dak yawa na cewa ana shirin tsige Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II sakamakon sauyin jam’iyya da Gwamnan Abba ya yi zuwa jam’iyyar APC.

Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun Gwamnan jihar Kano ne ya bayyana hakan ya ce babu wani shiri ko yarjejeniya da zai kai ga tsige Sarki Sanusi.

Ya yi nuni da cewa: “An naɗa Sarki Malam Muhammad Sanusi ne bisa doka bayan soke dokar masarautu, kuma babu wani shiri a matakin zartarwa na yin wani ƙarin gyaran.”

Ya tabbatar da cewa komawar Gwamna zuwa APC ba zai sauya halin da ake ciki ba ko kaɗan. “Sarki Sanusi zai cigaba da zama Sarkin Kano, babu wata niyya ta maye gurbinsa,” in ji shi.

Ya bayyana rahotannin da ke zagawa a matsayin jita-jita marasa tushe da mutane ba sa fatan alheri ga Jihar Kano ke haɗawa.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi kira ga al’ummar jihar Kano su yi watsi jita-jitar, sannan su gujewa yaɗa labarai marasa tushe.

  • Related Posts

    Rasuwar Audu Manaja Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Nijeriya -Sulaiman Hussain

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa a harƙar man fetur, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manaja, a matsayin babban rashi ga Arewa…

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Asibitin Ƙashi na Tarayya da ke Dala, Kano, ya ba wa ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi, Hon. Abba Kabir Bichi, lambar karramawa bisa gudunmawa…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Rasuwar Audu Manaja Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Nijeriya -Sulaiman Hussain

    Rasuwar Audu Manaja Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Nijeriya -Sulaiman Hussain

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

    LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala