Hon. Ibrahim Namadi Dala Ya Raba Babura Ga Magoya Bayansa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

A yammacin ranar Talata ne tsohon Kwamishinan Sufuri na jihar Kano kuma dan takar majalisar wakilai na karamar hukumar Dala, Hon. Ibrahim Namadi Dala, ya raba babura ga magoya bayansa.

Rabon baburan na daga cikin kokarin da yake yi na tallafa wa mabiyansa domin inganta rayuwarsu da bunkasa harkokin tattalin arzikinsu.

Tallafin ya samu yabo daga magoya baya da abokan siyasa. Sun bayyana shi a matsayin ci gaba da kula da walwalar mabiyansa da kuma kyakkyawar niyya ta basu damar samun rayuwa mai kyau.

Wadanda suka amfana da baburan sun nuna farin cikinsu. Sun ce tallafin ya zo kan lokaci kuma zai taimaka wajen saukaka zirga-zirga da karfafa harkokin kasuwancinsu.

Daga cikin matasan da suka amfana akwai Mustapha Kakisu, Abdul’aziz M. Sani, Zangina Gwammaja da Karibu Aminu.

Al’ummar karamar hukumar Dala sun kara jaddada kiran da suke yi ga Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya mayar da Hon. Namadi cikin majalisar zartaswar jihar. Suna ganin hakan zai karfafa kokarin da yake yi na tallafawa cigaban al’ummar Kano da kare muradun gwamnati.

  • Related Posts

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu sama da miliyan daya a faɗin jihar, a wani mataki da ta…

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a jam’iyyar APC kuma ɗaya daga cikin hadiman tafiyar siyasar Hon. Hassan Shehu Hussain, ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon.…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Dan’iya mourns attack victims, urges decisive action against insecurity

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    BOMBOY: Nasarar Samun Tikitin Takara Ba Tare Da Hamayya Ba Ta Gwamna Abba Da Hassan Hussain Ta Nuna Gamsuwar Al’umma

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Nasarar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na ADC, Nasara Ce Ga Masu Kishin Ci Gaban Ƙasa -Ambasada Mainasara Salga

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Gawuna Ya Zama Ɗan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar NDC

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya

    Sarkin Margunawan Kano Ya Taya Musulmi Murnar Sallah Ya Yi Kira Ga Kyautata Haɗin Kai Da Zaman Lafiya