Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hajiya Ruƙayya Sa’id Gwarzo, maiɗakin Alhaji Muktar Maude, wanda Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi, ya naɗa a matsayin Sarkin Gabas, ta bayyana matuƙar farin cikinta da godiya ga Allah bisa wannan babban matsayi da aka bai wa mijinta.
Hajiya Ruƙayya ta bayyana hakan ne a fadarsa bayan kammala bikin naɗin sarautar da aka gudanar a ranar Juma’a, inda ta ce babu abin da suke cewa face godiya ga Allah da ya tabbatar da wannan alheri a gare su.
Ta kuma miƙa godiyarta ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi, bisa wannan karamci da ya nuna musu, tare da addu’ar Allah Ya saka masa da alheri, Ya biya masa dukkan buƙatunsa na duniya da lahira.
Hajiya Ruƙayya Sa’id Gwarzo ta ƙara da cewa suna godiya ƙwarai ga al’umma da suka zo daga ciki da wajen jihar Kano domin halartar bikin naɗin sarautar, tare da taya su murna, wanda hakan ke nuna irin ƙauna da girmamawa da jama’a ke yi musu.
Ta bayyana cewa, a matsayinta na maiɗakin Sarkin Gabas, ta yarda da cewa zaɓin da Sarkin Kano ya yi wa mijinta ya ta’allaka ne da cancanta, domin mutum ne na jama’a, mai kyakkyawar zuciya, tausayi da taimako.
Ta ce mijinta na fifita buƙatar jama’a a kan tasa, inda zai iya sadaukar da nasa domin biyan ta wani.
Hajiya Ruƙayya ta kuma jaddada cewa, da yardar Allah, za ta bai wa maigidanta cikakken goyon baya da haɗin kai a dukkan al’amuran da suka shafi hidimar jama’a, tana mai godiya ta musamman ga al’umma da kuma abokan aikinta ‘yan jarida, kasancewarta ma’aikaciya a NTA, Kano.
A nata jawabin, Siddiƙa Maude, ‘yar’uwar Sarkin Gabas da aka naɗa, ta bayyana farin cikinsu matuƙa bisa dawowar wannan sarauta gidansu, inda ta ce sun san ɗan’uwansu mutum ne mai kyakkyawar mu’amala da jama’a da son taimako.
Ta ce ba su yi mamakin yawan jama’ar da suka halarci bikin domin taya su murna ba, kasancewar Sarkin Gabas mutum ne na mutane, kamar yadda mahaifinsu ma ya kasance, bisa tarbiyyar da suka samu tun suna ƙanana.
Siddiƙa Maude ta kammala da addu’ar Allah Ya ci gaba da ba Sarkin Gabas ikon kula da jama’a da ‘yan’uwansa, tare da yi masa jagora a wannan sabon nauyi da aka ɗora masa.






