Daga Ibrahim Muhammad Kano
Jam’iyyar NNPP ta zargi gwamnatin jihar Kano da ƙoƙarin musgunawa mambobinta, bisa zargin cewa ana ɗaukar matakai a kansu ne saboda sun ƙi amincewa su bi gwamnatin zuwa wata jam’iyya.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar a jihar, Injiniya Ibrahim Ƙaraye ya fitar, inda ya bayyana damuwar jam’iyyar kan wasu matakai da ta ce ba su dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin jihar Kano an zaɓe ta ne ƙarƙashin tutar NNPP, kafin daga bisani ta yi watsi da jam’iyyar, tare da komawa jam’iyyar APC.
Ta ƙara da cewa daga nan ne aka fara ɗaukar matakan da suka haɗa da janye kujerun aikin Hajji da aka ware wa wasu daga cikin mambobinta, ciki har da tsofaffin kwamishinoni, masu ba gwamnati shawara da kuma wasu shugabannin jam’iyya.
A cewar Ƙaraye, mutanen da abin ya shafa a matsayinsu na ‘yan jihar Kano suna da cikakken haƙƙin cin gajiyar irin waɗannan damammaki kamar yadda sauran al’umma ke yi.
Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnatin da matsa lamba da tsoratar da tsofaffin masu riƙe da muƙaman siyasa domin su mayar da motocin gwamnati da aka ba su lokacin da suke kan aiki, tana mai cewa motocin na daga cikin haƙƙoƙin da aka tanadar musu bisa hidimar da suka yi wa al’umma.
NNPP ta buƙaci gwamnatin jihar da ta dakatar da duk wasu matakai da ka iya tauye ko raunana ginshiƙan dimokuraɗiyya, tare da jaddada buƙatar gudanar da siyasa cikin mutunta juna da bin doka.







