Malam Haruna Ungogo Ya Ɗauke Mu Tamkar ’Ya’yansa –Farfesa Sarki Abba

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana yadda marigayi Malam Haruna Ungogo ya yi kyakkyawar hulɗa da kulawa ta musamman ga makarantar Sakandiren Kimiyya ta Dawakin Tofa, inda ya shugabance ta cikin hikima da jajircewa.

A cewarsa, a duk lokacin da yake shugaban makarantar, marigayin ba ya gajiya da zagayawa ajujuwa daban-daban, yana duba ɗakunan kwanan dalibai domin tabbatar da cewa komai na tafiya daidai. Wannan kulawa tasa ta sa ɗalibai ke jin an damu da su ƙwarai.

Farfesa Sarki Abba Abdulƙadir, tsohon ɗalibi a makarantar, kuma ɗan ajin 1984 ne, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ’yan jarida bayan gabatar da ƙasida da aka shirya domin tunawa da marigayi Malam Haruna Ungogo, wanda tsofaffin ɗaliban makarantar na ajin 84 suka shirya.

Ya bayyana cewa Malam Haruna Ungogo, malami ne mai hikima, musamman wajen zaɓen malamai da kuma tsarin koyarwa. “Duk da kasancewarsa ƙwararren Malamin Lissafi, yakan zaɓi ajujuwan da ɗalibai ke da rauni a darasin, yana shiga da kansa domin koyar da su har su fahimta,” in ji shi.

Farfesa Sarki Abba ya ƙara da cewa ajujuwan da ɗalibai suka riga suka ƙware a Lissafi, yakan damƙa su ga sauran malamai, domin ya fi mayar da hankali kan waɗanda ke buƙatar ƙarin taimako. “A sakamakon haka, ɗalibai da dama da ke da rauni a Lissafi sun samu ƙwarewa har suka ci jarabawa cikin nasara,” ya tabbatar.

Ya ce ba koyarwa kaɗai marigayin yake yi ba, har ma yana renon tarbiyya da gina tunanin ɗalibai, yana ƙarfafa musu gwiwa da ba su damar yarda da kansu. “Wannan tarbiyya ce ta sa ɗaliban makarantar suka shiga gasar kacici-kacicin ɗalibai na ƙasa ba tare da jin tsoro ko shakka ba, duk da kasancewar manyan makarantu masu dogon tarihi kamar King’s College, Legas, a gasar,” ya ce.

Farfesa Sarki Abba Abdulƙadir, wanda a yanzu yake zaune a ƙasar Amurka, ya ba da misali da wani abin tausayi da ya faru a lokacin ɗalibcinsa. Ya ce wata rana Malam Haruna Ungogo ya same shi yana barin makaranta saboda rashin lafiya, sai ya ɗauke shi a motarsa tare da iyalansa, daga Dawakin Tofa har zuwa Kano, inda ya sauke shi har kusa da gidansu a unguwar Makama.

Ya ce har yau ba zai taɓa mantawa da wannan karamci ba, tare da yadda marigayin ya ɗauke su tamkar ’ya’yansa. Har bayan sun gama makaranta, hulɗarsu da shi ta ci gaba, har ma lokacin da yake Ambasada, yana tuntuɓarsa ko yana Amurka domin neman shawarwari.

A ƙarshe, Farfesa Sarki Abba Abdulƙadir ya jaddada cewa Malam Haruna Ungogo ya rayu yana alfahari da ɗalibansa, shi ya sa suka ga ya dace su riƙa tunawa da shi, tare da ci gaba da kula da iyalansa da ya bari.

Ya ce bai kamata ɗalibi ya manta da malaminsa ba, ko yana raye ko bayan rasuwarsa ba, domin hakan na daga cikin ladabi da godiya.

  • Related Posts

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Daga Zubairu Lawal Babban Darakta Janar na NASEMA, Barrista Benjamin Akwash, ya gabatar da rahoton ayyukan shekara guda a Lafia, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da hukumar ta fuskanta.…

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Ƙungiyar WAZOBIA Conflicts Resolution and Peace Advocacy Initiative (WARCOPIA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada Garba Sulaiman Marafa (Marafan Lagos), ta gudanar da taron karrama wasu zaɓaɓɓun mutane da…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Shugaban NASEMA, Akwash, Ya Bayyana Ayyukan Shekara Daya

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    Sanya Bukatun Kano A Gaba Zai Haɗa Kan Jama’a -Bala Muhammad Gwagwarwa

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    ‘Ana Zargin Yunƙurin Ɓata Sunan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano’

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    Karramawar Da Aka Yi Min Sakamakon Kyakkyawar Tarbiyya Ce Daga Iyayena -Amb. Dakta Nana Maryam Gwambe

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    DSS Ta Saki Jami’an Gwamnatin Kano Kan Zargin Ɓata Sunan Kwankwaso

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani

    HARIN TA’ADDANCI A BUKKUYUM: Gwamna Lawal Ya Bayyana Shi Da Aikin Rashin Imani