Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jigo a jam’iyyar APC kuma Shugaban Jami’ar Siyasa ta Gangariya na ƙasa, Hon. Ado Tati, ya bayyana aniyarsa ta ba Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, cikakken goyon baya da gudunmawa domin bunƙasa ci gaban jihar Kano.
Hon. Ado Tati ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya koma jam’iyyar APC a ranar Litinin.
Ya ce ya yi matuƙar farin ciki tare da gode wa Allah da Ya nuna musu ranar da suka sake haɗuwa a tafiyar siyasa, yana mai bayyana cewa tun da daɗewa akwai kyakkyawar alaƙar aminci tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
“Ni da Gwamna Abba Kabir Yusuf muna da tsohuwar alaƙa ta aminci. Ba mu taɓa rabuwa da juna ba a mu’amala. Mutum ne mai sanin ya kamata, hangen nesa da girmama mutane,” in ji shi.
Hon. Ado Tati ya ƙara da cewa sake haɗuwarsu a tafiyar siyasa wata dama ce da za ta ƙara ƙarfafa haɗin kai, inda ya jaddada cewa zai ba gwamnan dukkan goyon baya da gudunmawar da ta dace domin ganin an samu cigaba mai ɗorewa a jihar Kano a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shugaba nagari mai aiki tuƙuru, kishin al’umma da siyasar fahimta, yana mai cewa dawowarsa jam’iyyar APC zai ƙara ba shi damar gina Kano, tare da haɗa kan al’ummar jihar baki ɗaya.






